Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamandan rundunar sojin sama NAF dake jihar Kaduna AɓM Abubakar Abdullahi ya ce rundunar ta samu nasarori da dama a yaƙin da take yi da ta’addanci a jihar Kaduna da yankin Arewa maso Yamma.
Abdullahi ya faɗi haka ne a taron da suka yi da Gwamna Uba Sani a ranar Asabar ɗin makon jiya a garin Kaduna.
Ya shaida cewa duk da ƙalubalan da suka yi fama da su shekarar 2024 shekara ce da rundunar ta samu nasarori a aiyukkanta na samar da tsaro a jihar.
Abdullahi ya ce a cikin shekarar da ya gabata rundunar ta rika kai wa ‘yan ta’adda hari ta sama da kasa kamar yadda dokar yaki ta gindaya.
Ya ce nasarorin da suka samu na da alaƙa da maida hankali da suka yi da haɗin gwiwar da suka yi da sauran jami’an tsaro a jihar.
Abdullahi ya tabbatar cewa nasarorin da suka samu ya karya gwiwowin ‘yan ta’adda da sauran masu aikata muggan ayyuka.
Ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da maida hankali domin ganin ta samar da tsaro don cigaba a jihar.
“Ina miƙa godiyata ga jami’an rundunar da sauran jami’an tsaron da muka haɗa hannu da su domin samar da tsaro a jihar.
Daga nan kwamishinan tsaro na jihar James Kanyip bayan ya jinjina ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen samar da tsaro ya yi kira gare su da su ci gaba da mai da hankali wajen gudanar da ayyukansu a jihar.
