Ribaɗu da wasu fitattun ‘yan Nijeriya sun bayyana cikin jerin mutum 100 mafi shahara a Afirka

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan tsaro, (NSA), Malam Nuhu Ribado da Fasto Enoch Adeboye mai kula da cocin Redeemed Christian, sun shiga jerin mutane 100 mafiya shahara da fice a nahiyar Afirka ta shekarar 2025.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa an saki jerin sunayen ne a ranar Lahadi inda wata ƙungiya mai suna Reputation Poll International (RPI), tare da haɗin guiwar takararta ta Global Reputation Forum, suka bayyana sunayen fitattun ‘yan Nijeriya.

NAN ta kuma rawaito cewa, wannan ƙiyasi ya kuma ƙunshi sunayen maza da mata daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka waɗanda suka yi fice a fannin fasaha da ƙirƙira da wasanni da aikin gwamnati da rahin kare muhalli da saurasu.

An ayyana Ribado ne saboda iya jagorancinsa wajen tafi da sha’anin tsaro ta fuskar haɗa kan rundunar sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro da cibiyar ba da bayanan sirri ta ƙasa wajen magance matsalar tsaro.

A kwanan nan ne ya jagoranci ceto wasu da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa da ke Nijeriya.

“Wannan wata hanya ce ta yaba wa ‘yan Afirka da suka yi fice wajen jajircewa da samar da cigaba.”

“An yi la’akari ne da tasirin waɗanda aka zaɓa a mataki na ƙasa da ma duniya bakiɗaya ta fuskar kawo wani sauyi mai ma’ana.”

“Karramawar shekarar 2025 ta yi la’akari ne da cikar kammala da kyakkyawan shugabanci da mai da hankali wajen cigaban al’umma.

Sauran waɗanda suke ƙunshe cikin wannan jerin sunaye akwai Dr Paul Enenche, wanda ya assasa cocin Dunamis International Gospel Church, da Cosmos Maduka, shugaban kamfanin motoci na Coscharis Motors da sanata Gbemisola Saraki.

A baya dai Enenche da Adeboye sun taɓa shiga wannan jerin sunaye, sai dai wannan shi ne karon farko da sunan Dr. Daniel Olukoya wanda ya assasa Mountain of Fire da Miracles Ministries, ya bayyana.

Sauran sun haɗa da: Bala Wunti, janar-manaja na zuba hannun jari a kamfanin man fetur na ƙasa (NAPIMS) da Tony Elumelu, shugaban bankin UBA da marubucin waƙa kuma mai waƙar ibada, Osinachi Egbu, wanda aka fi sani da “Sinach”.

Hakazalika, a cikin sunayen har da ɗan Najeriyan da aka haifa a Ingila, Olukemi Badenoch, wanda ke ɗan siyasa ne a ƙasar Ingila kuma shugaban jam’iyyar ‘yan ra’ayin riƙau (Conserɓatiɓe Party) tun watan Nuwabar 2024.

Sannan akwai zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana, John Mahama, wanda ya sake dawowa a karo na biyu, da Benedict Oramah, shugaban bankin Afreɗim da Mo Ibrahim, wanda attajirin ɗan kasuwa ne haifaffen Ingila ɗan ƙasar Sudan, na daga cikin waɗanda suka shiga jerin fitattun mutanen nahiyar Afirka.

Akwai kuma Isatou Ceesay ta ƙasar Gambia, wacce ita ma aka karrama da kuma ta yi fice wajen wayar da kan mutane kan sauyin yanayi da cigaba mai ɗorewa. Ta kawo cigaba mai yawa wajen tafi da shara da tallafa wa mata da bunƙasa tattalin arziƙin matan da ke karkara ta hanyar sarrafa robobin da aka yasar.

Ita ma, Karen Matsiko, wata ‘yar ƙasar Afirka ta Kudu ce da ta yi fice wajen harkar kuɗi da shugabanci da ake ganin ta kai wajen zama shugaba abar koyi a ɓangaren aikin banki da sufuri da ta fi mai da hankali ga abin da ya shafi kasuwanci ta la’akari da sabbin hanyoyi da ke ɓullowa.

Hakazalika, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan da Dr Jennifer Douglas, da Ogiame Atuwatse da sarkin Warri, duk sun samu shiga wannan jerin sunaye.

Sannan akwai fasto William Kumuyi, wanda ya kafa cocin da ake kira da General Superintendent of the Deeper Christian Life Ministry da Bishop Daɓid Oyedepo, wanda ya kafa kocin Liɓing Faith Church na daga cikin waɗanda aka karrama.

By ukarofi