Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da koyon karatun fasahar AI kyauta ga matasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na samar wa matasa ilimin fasahar zamani, Ma’aikatar Ƙirƙira da Kimiyya da Fasaha tare da haɗin-gwiwa da Sakatariyar Baitul Mali ta Commonwealth da Hukumar sadarwa ta Intel, ta ƙaddamar da makarantar koyon fasahar inganta harkokin komfuta ga matasa.

Ma’aikatar ta ce ilimin, wanda aka yi wa laƙabi da Artificial Intelligence (AI), zai bai wa matasan damar koyon karatun muhimman darussa da suka shafi fasahar AI, ƙa’idodin aiki, kayayyakin aiki da kuma yadda ake amfani da su a ko’ina a Duniya.

Haka kuma zai ba su damar zama wakilai game da fasahar da gudanar da shirye-shirye ƙarƙashin Intel da kuma samun ƙwarewa a fannin a zamanance.

An samar da shirin ne don inganta matasa game da samun damammakin ayyuka a nan gaba da jagoranci a harkar tattali na zamani gami da inganta ƙwarewarsu a ilimin AI.

Ma’aikatar ta ce waɗanda suke da ra’ayin shiga a dana da su, za su iya ziyartar shafi kamar haka; https://scienceandtech.gov.ng/academy

By ukarofi