Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da masu amfani da manhajar Tiktok ( Kungiyar Kwankwasiyya Tiktokers) waɗanda za su rinƙa tallata ayyuka da manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagorancin ƙaddamar da kwamitin a ofishinsa ranar Lahadi.
Kwamared Waiya ya ce an ƙaddamar da kwamitin ne duba da irin tasirin da manhajar Tiktok ta ke da shi a gurin al’umma da kuma taimakawa matasa masu amfani da shafin don samar musu da abin yi .
“Na farko waɗannan mutane za su tallata ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan kuma an samar masu aikin yi, kun ga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya”.
Ya ce za su haɗa kai da ƙwararru a fannin fasahar zamani domin su ba su horo na musamman domin su san dabarun isar da saƙo a manhajar ta Tiktok.
Da yake jawabi sabon shugaban ƙungiyar Shamsudden Abdullahi Sani ya godewa kwamishinan, sannan ya ba da tabbacin za su yi aiki tuƙuru domin tallata ayyukan gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ya ƙara da cewa “Tabbas Gwamnatin Jihar Kano tana aikin da ya kamata, mu kuma za su tsaya tsayin daka domin tallatawa da kuma wayar da kan al’umma kan manufofin gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf” inji Shamsudden
