Yadda gobarar tankokin fetur suka ci rayuka

Spread the love

Yadda gobarar Dikko Junction ta maimaita tarihi a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hatsarin wata motar tankar dakon man fetur akan hanyar Abuja, Babban Birnin Nijeriya, zuwa Kaduna ya haifar da asarar rayuka sama da 80, yayin da wasu da dama suka samu rauni. Wannan na zuwa ne ƙasa da shekara ɗaya bayan samun irin wannan hatsari a Jihar Jigawa da ke yankin Arewa maso Yammacin ƙasar, wanda shi kuma ya kashe kusan mutum 200. Irin waɗannan haɗurra na neman zama ruwan dare a Nijeriya duk kuwa da gargaɗin da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane ke ta yi.

Ana alaƙanta yawan samun hakan da rashin ingantattun hanyoyi da rashin bin dokokin hanya, sai kuma talauci da ke addabar al’umma.

A cikin watannin biyar da suka gabata a Nijeriya, an samu haɗarin tankokin mai a lokuta huɗu a faɗin ƙasar da suka yi sanadiyyar asarar rayuka 265, kamar yadda ministan yaɗa labaran Nijeriya, Muhamamd Idris ya bayyana.

Ga lokutan da haɗurran suka faru da kuma asarar rayukan da aka yi:

Suleja, Jihar Neja:

A ranar 18 ga watan Janairu ne hukumomi a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiya a Nijeriya suka tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 98 sakamakon fashewar tankar mai a garin Dikko da ke ƙaramar Hukumar Gurara a jihar Neja.

Sun kuma ce aƙalla mutane 55 da suka samu raunuka a hatsarin na kwance a babban asibitin Suleja da babban asibitin Sabon Wuse da cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke garin Dikko.

Wannan shi ne hatsarin tankar dakon man fetur na baya-bayan nan da ya girgiza ƙasar.

Taura, Jihar Jigawa:

A ranar 15 ga watan Oktoba 2024, hukumomi a jihar Jigawa sun tabbatar da cewa aƙalla mutane 181 ne suka mutu yayin da aƙalla 80 su ka jikkata sakamakon fashewar wata tankar dakon man fetur a garin Majiya na ƙaramar Hukumar Taura.

Babbar jami’ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa’adu, ta ce hatsarin ya faru ne ranar Talata da daddare bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.

A cewar ta hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.

Shi kuma kakakin rundunar ‘yan sanda a Jigawa, DSP Lawan Adam, ya ce bayan tankar ta faɗi sai mutane suka yi dafifi a wurin domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami’an tsaron da ke korarsu a ƙoƙarin kauce wa tashin gobara.

Shaidu sun faɗa wa manema labarai cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

Agaie, Jihar Neja:

Kwana ɗaya bayan fashewar tankar dakon man fetur a jihar Oyo, a ranar 8 ga watan Satumban 2025, aƙalla mutane 59 ne suka mutu bayan wata tankar mai ta yi taho mu gama da wata motar da ke ɗauke da mutane da kuma shanu.

Hukumar bayar da agaji ta jihar Neja ta ce haɗarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi wanda ya kai ga fashewar tankar da motar ɗaukan kaya da ma wasu motocin.

Egbeda, Jihar Oyo:

A ranar Asabar, bakwai ga watan Satumban 2024, wata tankar man fetur ta kama da wuta a kan titin Ibadan zuwa Ife a ƙaramar hukumar Egbeda da ke jihar Oyo wanda ya yi sanadiyyar ƙonewar motoci huɗu da wasu gidaje.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Mista Yemi Akinyinka ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar ta kama ne bayan mazauna yankin sun fara yunƙurin ɗibar man fetur ɗin da ke malelewa wanda ya kai ga mutane da dama sun samu raunuka, da dama kuma ya raba su da muhallansu.

An hana matasa ɗibar fetur bayan faɗuwar tankar mai a Taraba:

Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin matasa na ɗibar man fetur da ke tsiyaya daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jihar Taraba.

ɗaruruwan matasa ne suka yi tururuwa suna yunƙurin ɗibar fetur bayan faɗuwar tankar a kusa da Shatatetalen Mil 6 da ke Jihar Taraba, amma jami’an tsaro na Sibil Difens (NSCDC) suka hana su.

Faɗuwar tankar ke da wuya a ranar Laraba masu shaguna a wurin suka rufe suna tserewa saboda tsoron tashin wuta, amma matasan suka nemi zuwa su ɗebi man cikinta.

Kakakin Hukumar NSCDC na Jihar Taraba, Iliya Samuel, ya bayyana cewa zuwa jami’an hukumar a kan lokaci wurin ya taimaka wajen kawar da barazanar tashin wuta.

Iliya wanda ya ce an garzaya da direban motar da ya samu rauni a hatsarin zuwa asibiti inda aka duba lafiyarsa.

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar ya ce an ɗauki matakan da suka kamata a wurin da tamkar ta yi hatsari, domin daƙile duk wata barazana.

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan mutuwar sama sa mutanen 100 a yayin da suke kwasar fetur daga wata tanka da ta faɗi a Mahaɗar Dikko da ke ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja a kan Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A ranar Litinin wata mota mai ɗauke da mai ta faɗi a jihar, inda mutane suka yi rububin zuwa ɗibar man da ta ɗauko.

Shaidu sun ce mutanen sun yi zaton man fetur ne, amma sai suka ga ashe man girki motar ta ɗauko.

Gwamnan Neja ya hana manyan motoci bin gadar Dikko:

Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin kada wata mota da ta fito daga gadar Maje ta bi ta gadar Dikko.

Gwamna Mohammed Umaru Bago ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci wurin da wata tanka ta faɗi a kusa da mahaɗar Dikko, ƙaramar hukumar Gurara ta jihar Neja.

Gwamnan, wanda ya koka kan yadda wasu direbobin ke nuna halin ko-in-kula, ya ce dole duk wata mota da ta taho daga Maje ta bi ta gadar, sai dai su bi ƙarƙashin gadar su yi juyowa yadda ya kamata.

Ya kuma umurci babban kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya da ya kafa rundunar tsaro a yankin domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni, yayin da ya yi kira ga ƙungiyoyin sufuri da abin ya shafa da su ba hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa haɗin kai.

Bago ya bayyana fashewar tankar da ta salwantar da rayukan mutane da yawa a matsayin abin tausayi tare da godiya ga Allah da lamarin bai kai ga al’ummomin da ke makwabtaka da su ba.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin kammala hanyar Minna zuwa Suleja domin jinkirin aikin hanyar na ƙara janyo asarar rayuka da dama.

Gwamna Bago ya gode wa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Hukumar Kashe Gobara, Raod Safety, ƙungiyar Sufuri ta ƙasa (NURT) da sauran hukumomin da suka bayar da gudunmawa wajen kwashe waɗanda abin ya shafa.

Ya ce za a sake tura likitocin asibitocin Minna domin su taimaka wajen kula da waɗanda suka jikkata a halin yanzu suna jinya a babban asibitin Suleja.

By ukarofi