Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kebbi ta kama wani mai suna Muhammad Kado daga ƙaramar Hukumar mulki ta Koko bisa ga zargin kisan kai.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Sufurtandan ‘yan sanda Nafi’u Abubakar ranar Talatar da ta gabata.
Takardar ta bayyana cewa jami’an hukumar ne da ke aiki a ƙaramar hukumar mulki ta Koko/Besse suka kama Muhammad Sani wanda aka finsani da KADO da laifin harbe Al’Amin Garba ɗan shekaru tara da kuma Bello Shehu ɗan shekaru bakwai a garin Koko wajen bikin wani aure ranar sha huɗu ga watan Janairun shekarar nan.
Takardar ta bayyana cewa tuni dai Bello Shehu da aka harba a kai ya mutu shi kuma Aminu Garba yana asibiti yana samun kulawar likitoci.
Bayan kama Kado rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar gano bindiga ƙirar pistol ta gargajiya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bello M Sani ya yi Allah wadarai da wannan aikin inda ya yi kira ga al’umma musamman waɗanda ke riƙe da makamai ko waɗanne irin ne da su gaggauta hannanta su ga hukumar ‘yan sanda mafi kusa da su saboda tabbatar da tsaro da kuma kaucewa aukuwar irin haka.
Ya kuma bayyana cewa yanzu haka maganar tana sashen bincike na rundunar kuma in sha Allahu da zarar ta kammala binciken za ta gurfanar da shi kotu.
Wata mai kama da wannan haka-zalika kwamishinan ‘yan sandan jihar Bello M Sani ya yi kira ga ma’aikatar shari’a ta jihar da ta taimakawa rundunar ‘yan sandan wajen aiwatar da hukunci a duk lokacin da aka gabatar da ma su a gaban mashari’antu.
