Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Sarkin Malamai, Sheikh Kamalu Inuwa, babban limamin masallacin Hidaya da ke Kundila a birnin Kano, ya bayyana cewa kyawawan ɗabi’u irinsu, tausayi, kunya, kawaici, sanin ya kamata, kyauta, yafiya, afuwa ga wanda ya yi ma ba daidai ba bisa kuskure, da makamantansu na daga cikin kyawawan ɗabi’un Ma’aikin Allah (S.A.W), saboda haka siffatuwa da irin waɗannan siffofi daga ɗan Adam alama ce ta cewa ɗan adam na ƙaunar Annabi (S.A.W) ko da ba yi da’awa ba, amma ga mutum Musulmi ɗan Adam na cewa ya na ƙaunar Ma’aiki kuma a same shi da halaye akasin na Annabi, to akwai buƙatar ɗan adam ya tuba, ya yi aiki na nagarta da ƙoƙari wajen koyi da ma’aikin Allah duk da kasancewa babu wani wanda zai iya aiki irin na Manzon Allah tun da shi zaɓaɓɓe ne a wajen Mahaliccinsa, mahaliccin komai da komai kamar dai yadda Sheikh Kamalu Inuwa babba limamun masallacin Juma’a na Hidaya da ke Unguwar Kundila Gandu, ya bayyana a huɗubarsa ta sallar Juma’a da ta gabata.
Har ila yau ya bayyana cewa ƙaunar Ma’aiki wajibi ne kuma falala ce kuma alamar ƙaunar ma’aiki a zahiri da baɗini shi ne bin Allah da ƙauracewa saɓansa da aiki nagari a zahirinka da baɗilinka, Allah ya datar da mu.
Haka kuma babban limamin ya bayyana cewa wajibi ne zuciyar mumini ta cika da abubuwa guda biyu tsoron Allah da kuma tsoron azabarsa da kuma ƙauna da tsanani san rahamarsa a zuciyarsa wannan na daga cikin abun da zuciyar bawan Allah nagari ke tsaye a kanta ako yaushe abun da ake kira Alkaufu, Warraja. Wato tsananin a zabar Allah da tsananin kwaɗayin rahamarsa, waɗannan na ingiza barin saɓo kuma suna ingiza ɗa ‘a da bautawa Allah waɗannan abubuwa biyu.
A ƙarshe ya yi nasiha ga ɗaukacin shugabanni kan adalci, tausayi, amana, riƙon gaskiya, da kyautatawa al’umma, domin kasancewar gobe Alƙiyama za’a tambayi kowana shugaba aka irin mulkin da ya gudanar kamar yadda za’a tambayi kowa ne shugaba haka za’a tambayi kowane ɗan adam a wannan rayuwa ta duniya.
