Kammala wa’adin Bilkisu Dala a matsayin shugabar FIDA da zaɓen Salma Ahmad ya dace – Surajo Imam

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Dala Hon. Surajo Imam, ya bayyana cewa kammala wa’adin Hajiya Bilkisu Dala wacce ta shugabanci ƙungiyar lauyoyi mata ta ƙungiyar International Federation of Women Lawyers da ake kira FIDA ta kammala lafiya da manyan nasarori a zamanin shugabancinta cikin nasara, inda ya ce wannan ba ƙaramin abin farin ciki ba ne ga mutanen ƙaramar hukumar Dala da shugabancinta dama ɗaukcin ‘yan ƙungiyar da jama’ar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Hon. Surajo Imam ya bayyana haka ne a ƙaramar hukumar Dala jim kaɗan da miƙa ragamar shugabanci na ƙungiyar FIDA ta ƙasa reshen Jihar Kano, ga mai shari’a Hajiya Salma Ahmad ɗanbappha a matsayin sabuwar shugabar FIDA a ƙungiyar lauyoyi mata ta ƙasa reshen Jihar Kano, wanda aka gabatar a ƙarshen makon da ya gabata.

Haka kuma ya ƙara da cewa zaɓar mai shari’a Salma Ahmad ɗanbappha an yi daidai domin kuwa duk wata nasara da Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman shugabar FIDA da ta kammala wa’adinta ta samu da gudummawar mai shari’a Salma da sauran shugabannin ƙungiyar FIDA na ƙasa reshen Jihar Kano aka samu ya yi kuma alwashin cigaba da tallafawa ƙungiyar FIDA da sauran ƙungiyoyi da al’umma masu ƙoƙarin cigaban al’umma, a ko’ina.  

A nata jawabin Hajiya Bilkisu ta yi dogon bayani akan nasarori na kai FIDA inda ba ta kai ba a da, da taimakon Ubangiji da taimako ‘yan ƙungiyar musamman bin haƙƙin mata marasa galihu  a kotuna a kan matsaloli daban-daban tare da kyakkyawar fahimta da ma’aikatar shari’a ta Kano  da gwamnatin Kano da samar da Mujalla da ƙaddamar da ita wanda ya taimakawa wannan ƙungiyar da sauransu.

Ita ma sabuwar shugabar ƙungiyar Lauyoyi Mata, mai Sharia Salma Ahamad ɗanbappha ta bayyana wanan shugabanci a matsayin babban nauyi da aka ɗorata da yake buƙatar addu’a da goyon baya na ɗaukacin ‘yan ƙungiyar da sauransu.

Taron dai ya samu halartar manyan baƙi daga Kano da wajenta.

By ukarofi