Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shahararren malamin addinin Musulunci, Murtala Asada, wanda ke yawan sukar shahararren ɗan bindigar nan Bello Turji, ya tsallake rijiya da baya a gidansa da ke cikin garin Sakkwato.
Wasu mutane ɗauke da bindiga waɗanda suka rufe fuskokinsu ne suka kai masa hari inda ya yi musayar wuta da su kafin su tsare tsare daga gidansa.
ɗaya daga cikin makusantar malamin, Musa Lukuwa, a yayin da yake huɗubar Juma’a, cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata.
Ya ce, ‘yan bindigar sun yi nasarar haurawa gidan malamin bayan buɗe babbar ƙofar shiga gidan malamin.
“Cikin nasarar, malamin ya ga zuwan maharan ta na’urar kyamarar CCTɓ, daga nan ne ya fara harbin su da bindiga wanda hakan ya sa suka fasa abin da ya kawo su. Nan da nan suka bar gidan malamin.”
Daga nan ne ya buƙaci al’umma da su mallaki bindigarsu tare da samun izinin daga mahukunta domin kare kansu kamar yadda malamin ya yi.
A cewar wasu majiyoyi, maharan sun haura gidan malamin ne tare da kashe mai gadinsa, sai dai harbin malamin ne ya sanya su fasa abin da suka nufata.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata kungiyar mahara da ta ɗauki nauyin kai harin. Amma malamin da kuma Bello Turji sun sha fafatawa a kafafen sada zumunta na tsawon watanni inda Bello Turji ya buƙaci malamin ya bayyana inda yake zaune in ba tsoro ba domin su yi faɗa gaba-da-gaba.
Malam Asada a wani bidiyo da ya ɗau hankali a watan Satumbar bara, ya ƙalubalanci Turji kamar dai maigidansa, Halilu Sububu, wanda jami’an tsaro suka kashe kan aikata miyagun laifuka.
A yayin da yake mayar da martani ta wani saƙon bidiyo, Turji ya yi barazanar kashe malamin tare da zarginsa da rura rikici a maimakon samar da mafita.
‘Yan sanda a jihar Sakkwato, an rawaito cewa suna nazarin ɗaukar bidiyon kyamarar CCTV. Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Ahmed Rufa’i, ya ce, har zuwa yanzu dai ba a kai ga yi masa cikakken bayani ba kan lamarin ba.
