Gobe za a yi gagarumin Mauludin Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyas

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI

Mauludin bana, wanda ƙungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyas shine mauludi karo na 39 wanda ya yi daidai da shekarun Sheikh Ibrahim Niass shekara 125 kuma za a gudanar da mauludin a Kano. Gagarumin mauludi ne da ake shirya shi duk shekara don tunawa da Sheikh Ibrahim Niass da gabatar da wasu ayyuka na musamman da tunasarwa ga mabiya ɗariƙar Tijjaniya. A wannan shekarar, za a gabatar da Mauludin ne ranar 25 ga Janairu, 2025  a jihar Kano da yardar Allah. 

Tarihin Mauludin Shehu na ƙasa:

An fara gudanar da wannan mauludin a shekarar 1986 shekara 39 da suka wuce.

Waɗanda suka assasa mauludin:

‘Yan’uwa almajiran Sheikh Ibrahim Niass ne suka assasa wannan mauludi ƙarƙashin  jagorancin Marigayi Sidi Ahmad Kulaha wanda ya zama mataimakin shugaba da Sheikh Dahiru Abubakar Kurmi Shugaba, An fara da haɗuwa a yi karatun alƙur’ani duk lahadi anan ofishin Sidi Ahmad Kaulaha da ke Legas duk Lahadi. Yayin da ake yin wannan karatun sai wani ɗan’uwa ya zo ya gansu ya tambayi su “wannan me suke yi” suka ce “karatun Al-ƙur’ani  suke yi hadiyya ga Sheikh Ibrahim Inyas”.  Sai ya ce “Antu ma Majma’u Ahbab”. Daga nan ne ma wannan suna na ƙungiyar Majma’u Ahbab ya fito. Daga nan aka samu mutane haziƙai ƙarƙashin jagorancin Alhaji Garba Hamza da Sheikh ɗahiru Abubakar da Alhaji Talle da Alhaji Sani Rogo da Sheikh Aliyul Gali da Alhaji Aminu da saura da yawa suka ƙara ƙaimi da rungumar al’amarin . A nan aka  yi shawara a fara zaman mauludi. An fara wannan mauludi a Lagos duk shekara, tun ana yi a gida har aka fara yi a waje. Bayan likkafa ta ci gaba sai aka fara gudanar da Mauludin Shehu  a babban wuri  har ta kai an fara gudanar da mauludin a wajen jihar Lagos. A shekarar 1991 an yi  mauludin Shehu a jihar  Kaduna sai 1992 a Ibadan. A 1993  an yi a jihar  Kano. 1994 an kai mauludin Ilorin,  1995 aka yi a  Sakkwato. A shekarar  1996 aka je Osun 1997 aka je Filato haka dai aka yi ta tafiya ana zagayawa har shekaru huɗu baya aka yi a jihar  Bauchi da jihar jigawa da da Jihar Sakkwato. Shekarar 2022 an yi a jihar  Zamfara  a shekarar 2023 aka yi a jihar Kebbi sai kuma 2024 a birnin Tarayya Abuja. A yayin maulud na bara a Abuja shugaban Majma’u na ƙasa Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya isar da saƙon gwamnatin jihar Kano kan tana son a shekara mai zuwa a gudanar da Mauludin Shehu  a Kano kuma ƙarƙashin Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya Alh Dr Muhammadu Sunusi na biyu. Kuma daga baya aka sanar da amincewar yin mauludin a Kano. 

Yadda Mauludin Majma’u yake jiya da yau:

ƙungiya ta yi matuƙar albarka an samu cigaba a al’amuranta, duba da tun da aka fara yin Mauludin Shehu duk shekara ba a daina ba, ba a yi fashi ba,  kullum cigaba a ke samu ƙara haɓaka mauludin yake yi, ƙara tagomashi yake yi , mutane ƙara himma a hakar  suke yi, babu wani taro kowanne iri ne a ƙasar nan da yake tara jama’a  kamar mauludin Shehu wannan ba ƙaramar nasara ce ba masu gudanar da taron mauludin da masu halarta. Wani abun burgewa Tunda ake yin mauludin Shehu ƙarƙashin shugabancin ƙungiyar Majma’u babu wani abu na ɓatanci ko assha ko rashin jin daɗi da ya taɓa biyo bayan mauludin sai ma na san barka.Wannan ba karamar albarka ce ba. “Taron da aka fara a ɗaki da karatun alƙur’ani yau ana yinsa a jihohi wannan albarkace ta Shehu Ibrahim Kuma albarka ce ta almajiran Shehu Ibrahim. Wannan ƙungiya ta yi matuƙar albarka Sheikh Abdullahi Inyas ya sa mata hannu ya sa mata tambari  kuma ya sa hannu ya ba da izini akan mazaje jajirtattu irin su Sheikh ɗahiru Abubakar  da suka tsayawa ƙungiyar , wanda yake shugabantarta  tun a wannan shekarun har zuwa shekarar 2022 da Allah ya yi masa rasuwa.Allah ya saka masa da Alheri shi da Sidi Kaulaha” Inji shugaban Majma’u na ƙasa Sheikh Tijjani Sani Auwalu kuma kwamishina na Addinai na jihar Kano. 

Mauludin Shehu na ƙungiyar Majma’u yana da bambanci da saura:

Wannan mauludi na musamman ne , wanda ya haɗa kowanne ɓangare, kowanne ɗan zawiyya kowanne gidan Shehi duk an haɗu a inuwa guda. Kowanne Shehi yana zuwa wannan mauludi kuma in an zo mauludin kowa yana jin wannan maulidn nashi ne babu wariya. Wannan mauludi ya haɗe kowanne ɗan Tijjaniya kuma ɗan Faira Shehu Ibrahim wuri ɗaya don haka ana mauludin ne da yawu ɗaya. Duk Almajiran Shehu na haƙiƙa suna tare da wannan mauludin kuma suna zuwa da su da muridansu gabaki ɗaya,

Dalilan da suka janyo wannan nasara:

Dalilai da dama su suka haifar da wannan nasara da ake samu duk shekara yayin wanan maulud da majma’u take shiryawa amma daga ciki akwai: 

“ƙarfin almajiran Shehi Ibrahim Inyas suke da shi da yawan da suke da shi   da iya tara jama’a da tafiyar da su cikin amana da adalci  da haɗin kansu da soyayyarsu da iya mu’amalarsu shi ne silar wannan nasarar. Haka Goyon bayan da manyan Shehunnanmu suke bayarwa shi ma nasara ne. Don kuwa duka taron almajiran waɗannan shehunnan ne da masoya ke zuwa . Haɗin kai shi ma yana cikin ƙashin bayan nasarar wannna taron da ake yin a mauludi” Cewar tsoyon kwamishinan addinai na jihar Kano kuma malami a jami’ar Bayero ta Kano, Imam Dr Muhammad Nazifi Bichi. Taro ne da ke kawo cigaban al’umma, ba ma iya ‘yan ɗariƙar Tijjaniya ba ga dukkan musulmi. Taro ne da yake kawo cigaba a tattalin arziƙin ƙasa inda a wannan kwanakin da za a yin a taron al’umma daga ko’ina ciki da wajen ƙasar nan kan yi tururuwa don su halarta. Babu wani taro a cikin ƙasar Nijeriya da wajenta da yake tara ‘ya’yan Shehu bayan maulud ɗin Kaulaha, sai mauludin da Majma’u da take gabatarwa. “Tun zamanin Shehu Abdullahi tun ana zuwa mutum goma,  ishirin,  akwai shekarar da ta zo sai da muka zo da mutum tamanin da wani abun daga Kaulaha. Kuma duk shekara ne ‘ya’yan Shehu Ibrahim da jikoki da muƙaddamai da almajiran Shehu suna tasowa daga Sinigal su zo. Gwamnati tana samun damar ɗaukar wannan taro a mafi yawan lokuta  saboda kwadayin samun wannan albarka da Shehu Ibrahim don haka suke ba da gudummawa” Inji Sheikh Tijjani Sani Auwalu. 

Fatanmu:

Babban fatanmu a yi taro lafya a kammala lafiya a samu falalar da ake samu ta zumunci da tausayi da taimakon juna da ƙara jin wasu halaye na Sheikh Ibrahim Inyas da kuma fatan a yi aiki da duk abin da aka ji. Waɗanda suka rasu a wannan ƙungiyar da sauran almajiran Shehu,amin.

By ukarofi