Za mu ci gaba da kawo ayyuka nagari a Tarauni – Hon. ADS

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Dan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar Hukumar Tarauni Hon. Kabiru Dashiru Sule (ADS), ya bayyana ƙudirinsa na aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa da aka daɗe ba a taɓa ganin irinsu ba a yankin ƙaramar hukumar Tarauni.

Alh Kabiru Dashiru Sule ya bayyana wannan ƙudirin ne ta bakin tsohon sakataren mulki na ƙaramar hukumar Tarauni  Kabiru Sani Danbaris, a yayin ƙaddamar da aikin magudanan ruwa a layin mai Unguwa na mazaɓar Darauwa, wanda ɗan majalisar jiha ya samar a layin mai unguwa dake mazaɓar Daurawa a yankin ƙaramar hukumar Tarauni.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Tarauni Adamu Iliyasu Hotoro ya fitar ga manema labarai.

Ya ce Kabiru Sani Danbaris ya bayyana cewa wannan aiki na magudanan ruwa a mazaɓar Daurawa layin Mai unguwa wani ɓangare ne na shirye-shiryen da Alhaji Kabiru Dashiru Sule ADS ya sanya a gaba don tabbatar da ingantaccen yanayi da tsaftar muhallali ga al’ummar yankin.

Kabiru Danbaris Ya ce ayyukan raya kasa za su hada da gyaran tituna, gina makarantu, samar da ruwan sha mai tsafta, da kuma wasu ayyukan da za su taimaka wajen habaka rayuwar al’umma.

Ya ce ɗan majalisar jiha na ƙaramar hukumar Tarauni Kabiru Dashiru Sule ADS ya tabbatar da cewa yana nan daram a kan alkƙawarinsa na kawo sauyi da ci gaba ga yankin Tarauni, tare da tabbatar da cewa al’ummar yankin sun amfana da wakilcinsa, daganan ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa samar da yake bai wa ɗan majalisar jiha na kawo ayyukan raya ƙasa a faɗin yankin.

Da yake jawabinsa a yayin ƙaddamar da aikin shugaban ƙaramar hukumar Tarauni wanda ya samu wanilcin mataimakinsa Khalid Ayuba ya yi murna kan yadda ɗan majalisar jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni Kabiru Dashiru Sule ADS yake gudanar suna matukar alfahari inda ya ce aikin zai taimakawa al’ummar mazaɓar ta Daurawa dama yankin ƙaramar hukumar Tarauni. 

Khalid Ayuba ya yi kira ga al’ummar Tarauni da su cigaba da bai wa ɗan majalisar jihar haɗin kai da goyon baya domin ya cigaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa a faɗin yankin bakiɗaya.

ƙaddamar da aikin magudanan ruwan ya samu halartar shugaban jami’iyar NNPP na ƙaramar hukumar Tarauni Suleiman Muhammad Hogan da jagoran jami’iyar NNPP na ƙaramar hukumar Tarauni Injiniya Suleiman Sani, Mai bai wa Gwamna shawara kan ma’adanai da aikin noman rani Alh Aminu Abba da kuma kansiloli da masu bai wa shugaban ƙaramar shawara.

By ukarofi