An buƙaci Fulani su zama masu haɗin kai da zaman lafiya 

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Fulanin ƙaramar hukumar Badagiry dake cikin Jihar Legas, Alhaji Umar Mohammed Bello ɗan a salin jihar Neja dake Arewacin Nijeriya mazaunin garin Badagiri ta jihar Legas ya buƙaci al’ummar Fulanin yankin Badagiri da kewayenta gabaɗaya da su zama masu haɗin kawunan junansu tare da neman zaman lafiya a garin Badagiry baki daya.

Sarkin Fulanin Alhaji Umar Mohammed Bello ya buƙacin hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na taron bikin wankan sarautarsa ta Sarkin Filanin Badagiry da kewayenta gabaɗaya.

Taron bikin wankan sarautar ya samu halartar Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Mohammed Abubakar Bambado na biyu wanda ya samu wakilcin sarakunan fadar masarautar Fulanin jihar Legas da sarakunan Fulanin jihohin yankin Yarbawan wanda suka haɗa da jihar Ogun, Oyo, Ondo Osun, Ikiti da sauran waɗansu da suka fito daga waɗan su jihohin arewacin Nijeriya dama na ƙasashen da suka yi makwabtaka da Nijeriya baki ɗaya.

 Taron ya gudana ne a harabar fadar Sarkin Fuanin na garin Badagiry dake cikin jihar Legas, tun da farkon buɗe taro da addu’a a kana waɗan su daga cikin sarakunan Fulanin dama su yi tsokaci a wajen taron bikin wankan sarautar inda suka gabatar da muhimman jawabai daya bayan daya a ciki jawaban nasu har da kiraye-kiraye na neman haɗin kawunan junansu da kuma ba juna shawarwari ta yadda za su ƙara kokari a wajen sanya ‘ya’yayan su makarantun boko dama na a Arabbiya baki ɗaya ta wani ɓangaren kuma sun jin jinawa Gwamnatin Jihar Legas a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Babajide Sanwo Olu bisa ga ƙoƙarinsa na kawo ayyukan cigaban jihar tare da haɗa kawunan al’ummar jihar domin su cigaba da samun zaman lafiya a Legas da kewayenta gabaɗaya.

Shi ma a nasa tsokacin a wurin taron bikin wankan sarautar tasa ta Sarkin Fulanin ƙaramar Hukumar Badagiry da kewayenta gaba Alhaji Umar Mohammed Bello bayan ya kammala yi wa taro sallama irin ta addinin Musulunci sannan kuma ya cigaba da nuna jin daɗinsa dangane da yadda ya ga ɗumbin al’ummar Filani da Hausawa da sauran ƙabilu waɗanda suka zo taya shi murnar gabatar da wannan taro.

A kan haka ya cigaba da yi wa Allah Ubangiji godiya da ya ba shi damar gabatar da wannan taro tare da yi wa al’umma fatan alheri na komawar su gidajensu lafiya.

By ukarofi