An jinjina wa ƙungiyar haɗin kan Fulani ta ƙasa a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Daya daga cikin manyan mahautan jihar Legas dake babbar mayankar shanu ta abbatuwa Unguwar Okoba Agege cikin garin Legas wanda ake yi wa laƙabi da suna Alhaji Ado Araba Abakowa ya jinjina wa ƙungiyar haɗin kawunan Fulani ta ƙasa Kautal Hore a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Alhaji Bello Baɗejo dangane da ƙoƙarinsa na gudanar da jawaban da za su ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin Fulani da sauran al’ummar arewacin Nijeriya bakiɗaya babban mahaucin a Legas Alhaji Ado Araba Abakowa ya gabatar da wannan jinjinawar ce a ranar Asabar data gabata a lokacin da shugaban ƙungiyar ta Kautal Hore na ƙasa Alhaji Bello Badejo yake gudanar da jawabinsa a wajen taron ƙaddamar da shuwagabannin ƙungiyar na jihar Legas baki ɗaya.

Araba Abakowa ya ci gaba da cewa ya yi farin ciki dangane da jawabin shugaban, inda yake jawo hankulan Fulanin ƙasar nan cewar su guji aron halayen da ba nasu ba suna amfani da su a wajen gudanar da harkokin rayuwarsu, sannan kuma su zauna lafiya da kowa a Nijeriya.

Ya ce da sauran muhimman bayanai masu daɗi da shugaban ƙungiyar ya gabatar a wajen taron ƙaddamar da shuwagabannin ƙungiyar waɗanda za su ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin Fulani da al’ummar arewacin Nijeriya gaba ɗaya haka kuma Alhaji Ado araba abakowa ya cigaba dayiwa sabon shugaban Kungiyar ta kautel hore na jihar Legas Alhaji Bello mohammed Liman da matai makinsa nadaya Alhaji Magaji Bello da mataimakinsa na biyu Ahmed Suleiman Shanono fatan alheri dangane da wannan muƙamin da ƙungiyar ta basu kuma Allah Ubangiji ya tab batar da al’amarin.

 Haka zalika babban mahaucin a Legas Alhaji Ado Araba Abakowa ya cigaba shawartar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya duba da cewar farashin shanu da sauran dabbobi da suke yankawa domin amfanin al’ummar Nijeriya ya yi tashin gwauron zabi sakamako lalacewar kuɗin Nijeriya da ba su da auki a wajan canzasu su dawo dala ko kuma wadansu kudaden ƙasashen duniya a cewarsa.

By ukarofi