Ƙungiyoyin masu amfani da wayar salula sun ba gwamnati wa’adin janye ƙarin kaso 50

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyoyin masu amfani da wayar salula, National Association of Telecoms Subscribers (NATCOMS) da Association of Telephone, Cable TV, da Internet Subscribers of Nigeria (ATCIS), sun ba Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) wa’adin janye ƙarin kuɗin kira daga kashi 50% zuwa kashi 10% nan da ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025. Sun kuma soki ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kan shirin gudanar da zanga-zanga, inda suka nemi ta maida hankali kan kare haƙƙoƙin ma’aikata.

A cewar ƙungiyoyin, sun fahimci nauyin da ƙarin kuɗin ya kawo kan masu amfani da layukan sadarwa, musamman a wannan mawuyacin lokaci na tattalin arziki, amma sun yi kira da a daina ɗaukar matakan zanga-zanga da ba za su haifar da ɗa mai ido ba. Ƙarin kuɗin, wanda NCC ta amince da shi a ranar 20 ga Janairu, shi ne karo na farko tun shekarar 2013, inda aka ɗaga farashin kiran waya daga N6.40 zuwa N9.60 a minti daya, domin magance giɓin kuɗin da ake samu da kuma tsadar gudanar da ayyukan kamfanonin sadarwa.

Shugaban NATCOMS, Adeolu Ogunbanjo, ya bayyana cewa suna tattaunawa da NCC kan buƙatar rage kuɗin zuwa kashi 10%, kuma suna sa ran samun amsa daga hukumar a mako mai zuwa. Ya ƙara da cewa, “Mun miƙa ƙorafin mu ga NCC, kuma mun basu lokaci su amsa mana. Amma idan har zuwa Laraba ba su mayar mana da martani ba, za mu wallafa sanarwa da ke ɗauke da bayanan tattaunawar mu, sannan mu ɗauki matakin shari’a cikin kwanciyar hankali da lumana.”

Ogunbanjo ya kuma yi kira ga NLC da ta kaucewa ɗaukar matakai da za su kawo cikas ga kamfanonin sadarwa, inda ya ce, “Kamfanonin sadarwa kasuwanci ne masu zaman kansu, ba hukumomin gwamnati ba. Dole ne a kare su daga matsalolin da ke shafar harkokin su. Ya kamata NLC ta nemi hanyoyin da za su tabbatar da adalci ga masu amfani da layuka da kuma kamfanonin sadarwa.” Ya kuma jaddada cewa, duk da ƙarin kuɗaɗen shiga da ake samu daga masu amfani da layukan sadarwa, kamfanonin suna fama da ƙaruwar kuɗaɗen gudanarwa saboda hauhawar farashi, sauyin darajar Naira, da kuma manyan jarin da ake yi domin biyan buƙatun masu amfani da sadarwa a ƙasar.

By ukarofi