Daga USMAN KAROFI
Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya musanta zargin cewa Sojojin Najeriya sun yi tilastaccen zubar da ciki ga matan da ‘yan Boko Haram suka yi wa ciki a Arewa maso Gabas.
A cikin rahoton Reuters na watan Fabrairun 2022, an zargi sojojin da gudanar da wani sirrin shirin zubar da ciki domin yaƙar ƙungiyoyin ta’addanci a Arewa maso Gabas, inda aka ce an zubar da aƙalla jariran mata 10,000 a wannan shiri. Sai dai, yayin wata hira a shirin Politics Today na Channels Television, Janar Musa ya musanta wannan zargi, yana mai bayyana cewa wasu ƙungiyoyi NGO ke da hannu a wannan labari don ɓata sunan Najeriya.
“Lokacin da suka kawo wannan zargi, na ji ba daɗi saboda mafi yawan ƙungiyoyin nan ba sa fatan alheri gare mu,” in ji CDS. “Mun kafa kwamitin bincike mai zaman kansa ta hannun hukumar kare haƙƙoƙin ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), kuma babu wata hujja da ke tabbatar da wannan zargi.” Ya ƙara da cewa, “Mun ba kwamitin cikakkiyar damar bincike na tsawon shekara guda da rabi, kuma sun kammala rahotonsu tare da wanke sojoji daga kowanne laifi.”
Janar Musa ya ce, gwamnati ta nemi babban Llauyan Ƙasa ya kai ƙarar masu yaɗa wannan zargi zuwa kotu don neman afuwa a bainar jama’a. Ya kuma zargi wasu NGO da gudanar da shirin zubar da ciki ga ‘yan Najeriya sama da 10,000, wanda ya iya zama tushen wannan zargi da aka yaɗa. “Idan har suna zargin mu, kuma muna aiki da ƙungiyoyin Ƙasa da ƙasa da kuma na gida, suna nufin duka ba mu san abin da ke faruwa ba?” in ji shi.
