Ƙungiyoyin Arewa da na ƴan gwangwan sun roƙi Wike ya dakata da rusau a kasuwar Fanteka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An bayyana rushe kasuwannin Fanteka a wasu yankunan birnin tarayya Abuja da Minista Nyesom Wike ke yi a matsayin amfani da laifin wani wajen ƙuntata wa wasu.

Kodinetan ƙungiyar Arewa ta ‘Arewa Renaissance Group’, Umar Abba ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci wasu kasuwannin gwan-gwan da aka rushe su a unguwannin Deidei, Karmo, Kabusa da wasu wurare a babbar birnin.

Ya yi magiya ga Minista Wike da ya dakatar da rusau da ya ke yi wa kasuwannin, inda ya ce hakan zai taimaka wajen samun ƙaruwar marasa aikin yi tare da ƙarfafa ayyukan sata acikin masu irin sana’ar da aka nakasa.

Kasuwannin Fanteka da ake yin sana’ar gwan-gwan acikin su, sanannu ne a jihohin Arewa kamar su Kano, Kaduna, Filato da sauransu.

Ya ƙara da cewa, yayin da aka samu masu satar kayan amfanin jama’a ko lalata su, hakan ba shi ke nuna cewa baki ɗayan su haka suke ba.

Kodinetan ya kuma roƙi Ministan da ya ba su dama ta biyu ganin yadda al’umma ke fuskantar halin matsin rayuwa, ya na mai cewa ƙungiyarsu ta na yin duk mai yiwuwa wajen shiryawa da wayar da kan mambobin harkar akan abinda ya shafi satar kayayyakin ababen more rayuwa.

Kazalika, ya nemi ministan da ya yi musu gayyata ta musamman don shirya yadda za a shawo kan matsalar, ya na mai cewa yayin da mafi yawancin al’umma suke ƙoƙarin dogaro da kansu, akwai buƙatar a ƙarfafa musu gwiwa.

Daga ƙarshe, ya jinjina wa ministan bisa namijin ƙoƙari da ya ke yi a jagorancinsa, ya na mai masa alƙawarin za su cigaba da kiyaye doka da oda.

By Babaji