
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Asabar ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce jami’anta a sassa daban-daban na ƙasar sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda guda 79 da kuma kama wasu 224.
Ta kuma ce jami’ai a Rundunar Atisayen Arewa ta Tsakiya sun kashe sanannen Kwamandan ƴan bindiga mai suna Abu Mosaje a ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.
Daraktan Yaɗa Labarai na hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami’an sun kama wani shahararren mai garkuwa da mutane da ake kira Babangida Gora Usman a ƙaramar hukumar Sanga, a jihar Kaduna.
Ya ce hakan na zuwa ne a ƙoƙarin sojoji na dakatar da ayyukan ta’addanci da suka dabaibaye sassan ƙasar.
Ya ƙara da cewa Atisayen jami’an, ba iya ƴan ta’adda suke hari ba, har ma da masu taya su, kamar ƴan tsegumi da masu tallafa musu.
Manjo-Janar Buba ya kuma ce sun kama ɓarayin albarkatun mai guda 28 da suka saci wanda kuɗinsa ya kai kimanin Naira miliyan 747.07 da ceto mutane 67 da aka yi garkuwa da su.
Bugu da ƙari, sojojin sun gano tare da ɗaiɗaita wuraren dafa ɗanyen mai guda 215 da ramuka 26 da kwale-kwale 29 da tankokin ajiya 62 da duro 20 da kuma haramtattun wajen tace mai guda 42.
Har’ilayau, sun ƙwato wasu abubuwa da ke taimaka wa ayyukan ɓata-garin da suka haɗa da babura 21, motoci 2 wayoyin salula 11 da dai sauransu.
Kazalika, jami’an sun kuma ƙwato muggan makamai guda 104 da alburusai 1,953 daga hannun ƴan bindiga.
Daga ƙarshe, ya ce dakarun za su cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci da ke addabar sassa daban-daban na faɗin ƙasar.
