
Daga BELLO A. BABAJI
An zargi manyan abokanan hamayya a rikicin siyasar Ribas, wato Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar da ƙin gaisawa da juna a lokacin da suka gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata.
Jagororin biyu suna daga cikin tawagar Ogoni, wadda ta ziyarci Shugaban ƙasar don tattauna batun yiwuwar dawo da samar da mai a yankin ‘Ogoniland’.
Wata majiya daga zaman ta ce duk da cewa an hango sun ɗauki hoto da Shugaba Tinubu, amma ba su yi musabaha ko rungumar juna ba, kaɗai sun yi abinda ya kai su ne, inda bayan kammala zaman, sai aka ga kowa ya kama gabansa.
Ta ce Wike ya zo Fadar shugaban ƙasar ne daga wani waje da ake gudanar da wasu ayyuka, wanda ana yin hoton tawagar, sai aka ga ya kuma wajen aikin nasa.
Majiyar ta ce Shugaba Tinubu bai yi tsokaci game da rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara ba, inda ya mayar da hankali akan abinda ya sa aka kira zaman.
A makon da ya gabata ne aka ga Wike ya na jaddada matsayarsa ta cewa ba zai sasanta da Fubara ba matuƙar an cigaba da rikicin, kamar yadda ya bayyana a wata hira da wani gidan talabijin.
Saidai, Ƙungiyar Dattawan yankin Neja-delta (PANDEF) ta samar da kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Obong Victor Attah don shirya zaman tattaunawa da zai sasanta tsakanin ƴan siyasar biyu.
