Shettima ya halarci ɗaurin auren ‘yar Ibrahim Abuna a Maiduguri

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya halarci ɗaurin auren Aisha, ‘yar Hon. Ibrahim Abuna, ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Mafa, Dikwa, da Konduga a Majalisar Wakilai, a Maiduguri, Jihar Borno.

Bayan isowarsa a sansanin sojojin sama na Maiduguri, an tarbe shi cikin girmamawa daga al’ummar Borno da wasu manyan baƙi. Daga nan ya wuce gidan Hon. Ibrahim Abuna da ke Commissioners’ Quarters, GRA, inda aka gudanar da ɗaurin auren.

Daurin auren ya gudana ne a gidan iyayen amaryar, inda Sanata Ali Modu Sheriff ya tsaya wa amarya, yayin da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya tsaya wa ango, Mohammed.

A wajen taron, akwai manyan baƙi da suka haɗa da ‘yan majalisar wakilai, ƙarƙashin jagorancin bulaliyar majalisa, Usman Kumo, tare da sauran mambobi 38. Hakazalika, Sanata Kaka Shehu Lawal, ministan noma da tsaron abinci, Sanata Abubakar Kyari, da kakakin Majalisar Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, sun halarta tare da sauran mambobin majalisar jiha da kuma mambobin majalisar zartarwa ta jihar. Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (Arewa), Hon. Ali Bukar Dalori, shi ma ya kasance wajen taron domin nuna farin ciki tare da iyalan.

By ukarofi