
Daga BELLO A. BABAJI
Rahotanni sun nuna cewa baƙin haure a Amurka daga Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka sune waɗanda gwamnatin ƙasar za ta kora nan ba da jimawa ba.
Hakan ya haifar da tsoro acikin ƴan Nijeriyan da ke zaune a ƙasar, bayan da zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, Donald Trump ya shelanta yaƙar baƙin haure da ke zama a Amurka ba bisa ƙa’ida ba.
A ranar rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar na 47 ne Trump ya sanya hannu akan dokokin da ke tsawwala matakan zama a ƙasar, waɗanda daga ciki akwai batun hana zama ƴan ƙasa ga yaran da aka haifa a ƙasar daga waɗanda ke zaune a ƙasar ba bisa doka ba.
Aƙalla ƴan cirani marasa rajista guda 538 ne aka yi waje da su daga ƙasar a ranar Alhamis.
Sakataren yaɗa labaran Shugaba Trump, Karoline Leavitt a shafinta na X, ta ce za a fitar da mutane daga Amurka masu yawa a tarihin ƙasar nan ba da jimawa ba.
Saidai, a yayin da Shugaban ƙasar ya ɗauki matakin, ƴan Nijeriya da dama da ke zaune a unguwanni daban-daban sun koka game da hakan, a inda suka shiga fargabar fuskantar kora daga ƙasar.
Hakan na zuwa ne ganin yadda Trump ya fara sallamar ƴan ƙasashen Mexico, Haiti da Indiya waɗanda a yanzu aka mayar da hankali akansu, yayin da kuma ake hasashen ƴan Afrika sune sahu na gaba.
Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa ƴan Nijeriya da dama suna ƙoƙarin takaice zirga-zirgarsu.
Wani mai suna Adebayo daga birnin New York ya bayyana cewa a halin yanzu al’umma sun damuwa a unguwannin da ƴan Nijeriya suke zama wanda ya gefa da dama daga cikinsu shiga halin zaman ɗar-ɗar.
