
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Malamin Addinin Islama a Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya shawarci gwamnati da ta bai wa matasan Kudu-maso-Gabas horo ta yadda za su magance rikici Mutanen Biafra na IPOB.
A wata hira da Blueprint, Sheikh Gumi ya ce mafi dacewar hanyar magance matsalolin ta’addanci a shiyyar ita ce bai wa matasan da suka san yadda yanayin ta’addanci ya ke a yankin horon da za su iya tunkararsa.
Ya bada misali da Asari Dokubo da Tompolo a yankin Neja-Delta, waɗanda suka sauya daga ubannin daba zuwa masu kare harkokin gwamnati da yaƙar manyan ƴan ta’adda.
Ya ce amfani da ƙarfin soja a wuraren da ke da yawan fararen hula wajen yaƙar ta’addanci ya kan haifar da rasa rayukan waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, wanda ba hakan aka so ba.
A madadin haka ne ya yi kira ga jihohi a Arewa da su gudanar da tattaunawar sulhu da ƴan bindiga a matsayin hanyar wanzar da zaman lafiya a shiyyar.
