



Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Babban Kwamandan Runduna ta 1 ta sojojin Najeriya dake Gusau, Burgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan Bello Turji a matsayin matsoracin da a kodayaushe ya ke ɓoyewa don tsoron hare-haren da sojoji ke kai wa a sansanin ƴan ta’addan da suka addabi yankunan Jihar Zamfara.
Burgediya Janar Timothy ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai jim-kaɗan bayan kammala bikin ƙungiyar Sojojin Nijeriya ta West African Social Activities (WASA) na 2024 da aka gudanar a Gusau ranar Asabar.
Burgediyan ya kuma ƙalubalanci jiga-jigan ƴan ta’adda musamman Bello Turji da mayaƙansa, da su fito daga maɓoyarsu, su tunkari sojoji idan sun isa a maimakon ɓoyewa da suke yi.
“Mun tabbatar da Bello Turji da mutanensa matsorata ne. Ina ƙalubalantar su da su fito fili idan da gaske suke yi maimakon su ɓoye kansu, su ga abin da zai faru da su, kuma ina son in shaida wa Bello Turji cewa, tsoronsa ba zai kuɓutar da shi ba kuma nan ba da jimawa ba za mu kakkaɓe shi da mutanensa baki Daya”, inji Janar Timothy.
Ya ƙara da cewa, “Turji matsoraci ne kuma ya yi watsi da sojojinsa saboda farmakin da sojoji suka kai masa tare da masu yi masa biyayya, kuma Alhamdulillahi mun samu gagarumar nasara wajen kawar da da yawa daga cikin waɗannan ‘yan ta’adda kuma za mu yi ƙoƙarin ganin mun cigaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a maɓoyarsu daban-daban domin samun zaman lafiya a Zamfara da Arewa maso Yamma baki daya.”
Janar Timothy ya jaddada aniyar rundunar soji na fatattakar duk wani nau’in ta’addanci domin samar da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
Burgediyan, wanda ake yi wa laƙabi da “Jar Kunama” ya yaba wa al’ummar Zamfara bisa haɗin kan da suke bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaƙi da ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.
Ya yi kira ga sojoji da su cigaba da jajircewa da kishin kasa wajen yaƙar ‘yan ta’adda domin tabbatar da yankin Arewa maso Yamma ya samu zaman lafiya mai ɗorewa.
Hakazalika, wakilinmu ya ruwaito cewa, taron WASA na shekarar 2024 da sojojin Najeriya suka gudanar a jihar Zamfara ya ƙayatar matuka, inda ƙungiyoyin al’adu daban-daban irin su Hausawa, Tiv, Igbo, Yarbawa da ƙungiyar mafarauta (Yan Tauri) suka baje kolin basirarsu wanda ya jawo hankali tare da nishaɗantar da manyan baƙi a yayin taron.
