
Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Kamar yadda binciken UNICEF ya nuna, daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi sakamakon ambaliyar ruwan sama ta raba da muhallansu a ƙasashe 85 a duniya a shekarar 2024, ɗalibai miliyan 2.2 ne a Nijeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin karatukansu a shekarar da ta gabata kamar yadda rahoton ƙungiyar Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya bayyana.
Da ya ke gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta auku a Jigawa a shekarar da ta gabata ta lalata gine-ginen makarantu 115, wanda hakan ya kawo cikas ga ɗalibai masu yawa a faɗin jihar.
Ya kuma bayyana alhininsa kan yadda lamarin ya haifar da tsawaita rufe makarantu, wanda ya shafi karatun yara sama da 92,518 a kananan hukumomi 27 na Jigawa.
“Hakan ya haifar da tsawaita rufe makarantu da kuma rashin wadatar ilimi ga dalibai kimanin 92,518, wadanda 43,813 daga cikinsu mata ne, yayin da 48,705 kuma yara maza ne, a faɗin kananan hukumomi Jihar 27”, inji Mista Farah.

Ya yi nuni da cewa, UNICEF, tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin ƙasashen waje da na kungiyar kasashen renon Ingila da ke, na tallafa wa gwamnatocin Jihohin Kano da Jigawa don samar da yanayin koyo da koyarwa mai kyau domin rage tasirin sauyin yanayi da ya shafi koyon ilimi a makarantu.
Ya kuma ce a shekarar 2024, UNICEF ta ɗauki nauyin matasa dubu ɗaya, waɗanda 350 daga cikinsu sun fito ne daga Jigawa, yayin da 650 kuma suka fito daga Katsina, don dasa bishiyu 300 a yankin hamada da kuma wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa a jihohin biyu, domin daƙile tasirin sauyin yanayi a yankunansu.
Shugaban na UNICEF ya kuma bayyana cewa a shekarar da ta gabata asusun ya gina cibiyoyin kula da tsaftar ruwa da tsaftar muhalli (WASH) a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a wuraren da ake buƙata a cikin jihohin uku.
Kazalika, ya ce asusun ya kuma gina wasu ajujuwa tare da gyara wuraren tsaftar muhalli a makarantu 33, inda aka gina 25 a Kano, sauran 8 kuma a Jigawa, waɗanda yara 39,432 ke amfani da su a jihohin biyu.
