
Daga BELLO A. BABAJI
Hedikwatar Tsaron Nijeriya a Abuja, ta ce jami’an sojoji na atisayen Haɗin Kai sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin ƴan ta’adda da wasu mambobinsu sama da guda 70 a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
Daraktan yaɗa labaran Hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a inda ya ce dakarun Operation HAƊIN KAI da ke aiki a Arewa maso Gabas a wani yanki da ake kira Timbuktu Triangle da ƴan ta’adda suka mamaye, sun kai farmaki da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin ƴan ta’addar.
Ya ce sun fara gudanar da atisayen na musamman ne tun a ranar 16 ga watan Junairu, wanda hakan ya kai ga sun shafe ƴan ta’adda 70 da kwamandojinsu guda uku daga yankin a yayin gumurzun.
Ya kuma bayyana sunayen kwamandojin ƴan ta’addar kamar haka: Talha, Kwamandan mayaƙa na musamman; Malam Umar, Kwamandan ayyukan mayaƙa; da kuma Abu Yazeed, wanda shi ne Kwamandan Birget.
Manjo-Janar Buba ya ƙara da cewa, a lokacin da jami’an suke gudanar da atisayen, mayaƙan ƴan ta’addar sun dasa boma-bomai a hanyoyin da dakarun sojojin suka bi wajen kai farmakin da kuma sanya wasu ababen fashewa a motoci don kariya.
Saidai, duk da ƙoƙarin sojojin na katse shirin mayaƙan ƴan ta’addar, sai da aka samu 22 da suka rasa rayukansu tare da raunata wasu da dama da ababen fashewar suka yi.
Har’ilayau, rundunar tsaron ta ce za ta fitar da sauran bayanai game da sojojin da suka jikkata da waɗanda suka mutu, ta na mai kira ga gidajen jaridu da su ƙaurace wa yaɗa sunayen jami’ai ba tare da sanarwa ta musamman daga gare ta ba.
