
Daga BELLO A. BABAJI
A safiyar ranar Lahadi ne wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a garin Garo dake ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano, inda suka yi garkuwa da wata matashiya mai suna Zainab bayan karɓar Naira miliyan 8 daga hannun iyalanta.
Wani shaida ya ce wasu ƴan fashi guda goma ne suka hari gidan wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Auwal, a Garo Sabuwar Unguwa da misalin ƙarfe 1:20 na dare.
Ya ce uku daga cikin su na ɗauke da bindigu yayin da sauran kuma suka riƙe wasu makamai.
An ruwaito cewa a yayin shiga gidan ne, ƴan bindigar suka karya wata ƙaramar ƙofa, inda suka tara mutanen gidan a waje guda tare da razana su da makaman nasu.
Shaidan ya ƙara da cewa, mai gidan ya nemi tattaunawa da ƴan bindigar don kare iyalansa daga cutarwa, inda suka buƙaci ya ba su kuɗaɗe, wanda a nan take ya damƙa musu miliyan N8.
Saidai, bayan karɓar kuɗin ne a yayin ficewarsu daga gidan, sai suka tasa ƙeyar babbar ƴarsa, wadda ta gama karatun boko na matakin sakandare.
Kawo yanzu ba a san inda matashiyar take ba kasancewar ƴan fashin ba su tuntuɓi iyalan nata ba.
Lamarin ya haifar da tsoro acikin al’ummar yankin inda suka yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki don ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.
A lokacin da aka yi ƙoƙarin ji ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda kuma ya ce sun aika tawagar bincike don kamo waɗanda ke da hannu a ciki.
