’
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin ɓarayin dabbobi a ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe da satar awaki da tumaki 85.
Waɗanda ake zargin sune, Abdulkadir Tukur mai shekara 35 da Ibrahim Saidu mai shekara 20, kuma an kama su ne bayan an kama su da tumaki 28 da awaki 57 wanda jimillar su ta kai 85 kuma ake kyautata zaton na sata ne.
Rundunar yan sandan jihar tace a ranar 25 ga Janairu, 2025, ne bayan rahoton da dagacin garin Tulmi, Abubakar Umar, ya bayar kan wasu dabbobi da aka sace a yankin. Yayaji Muhammad, wani mamba na ƙungiyar mafarauta ta Tulmi, ya tare waɗanda ake zargin a kan hanyar shanu na Tulmi yake bincikar su suka kuma kasa bada amsa gamshahhiya kan dabbobin da ke hannunsu.
A wata sanarwa da DSP Buhari Abdullahi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Gombe, ya fitar ta bayyana cewa jami’an sashen ‘yan sanda na garin Pindiga sun fara bincike kan lamarin, inda waɗanda ake zargin suka amsa cewa sun aikata laifin sata ne, kuma daga cikin dabbobin da aka gano, awaki 25 ne an kuma riga an miƙawa masu su.
Masu dabbobin da aka gano sune Joseph Ahmadu da yake da awaki shida da Bello Sintali awaki huɗu da Godwin Iro awaki 10, da Zaraya Jepter awaki biyar da suka fito daga ƙauyukan Jurara, Kashere, da wasu yankunan ƙaramar hukumar Akko da Billiri.
Haka kuma, DSP Buhari ya bayyana cewa ana neman wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a laifin masu suna Rabe Saidu, Hamisu Saidu, Bode Saidu, da Wada Saidu, wadanda dukkansu ke gudun hijira. Ya ce ana ci gaba da ƙokarin cafke su tare da dawo da sauran dabbobin da aka sace.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe ya yaba da ƙoƙarin mazauna yankin wajen bayar da rahoton abubuwan da ake zargi.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura, tare da kai rahoto cikin gaggawa ga ofisoshin ‘yan sanda mafi kusa domin tabbatar da tsaro a jihar.
