Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da sanya ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa ƙasar Biyafara ta IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

A wani mataki na bai-ɗaya da kwamitin mutane uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Hamma Barka ya yanke, Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wanda ya haramta ƙungiyar ta IPOB.

Kotun ta ce, ba ta samu dalilin yin watsi da ra’ayin Gwamnatin Tarayya a kan ƙungiyar ba.

A cewar kotun, Gwamnatin Tarayya ta yi aiki bisa doka ta hanyar haramta ƙungiyar da ayyukanta baki ɗaya da ke barazana ga tsaro da ci gaban ƙasa.

Ta warware duk wasu batutuwan da suka shafi ƙungiyar ta IPOB tare da yin watsi da ƙarar da ƙungiyar ta shigar na rashin cancanta.

Marigayi tsohon alƙalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a Abdul Abdu-Kafarati, ya yanke hukuncin da ya yanke a ranar 15 ga Satumba, 2017, ya haramta ayyukan ƙungiyar IPOB a Nijeriya.

Hukuncin haramcin ya biyo bayan wani ƙudiri da tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Mister Abubakar Malami ya shigar a madadin gwamnatin tarayya.

Musamman, mai shari’a Kafafati ya bayyana a matsayin haramtacce, duk wasu ayyukan ƙungiyar musamman a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu na ƙasar nan.

Ya kuma hana “kowane mutum ko rukuni na mutane shiga cikin kowane irin ayyukan ƙungiyar”.

Alƙalin ya umurci Ministan Shari’a da ya tabbatar da cewa ya buga odar haramcin a cikin kundun hukuma, da kuma a cikin jaridu biyu na ƙasa.

By ukarofi