Wata mata a Faransa wadda ta daina amincewa da mijinta ta samu nasara a wata shari’a da aka tafka a kotun kare haƙƙin bil’adama ta nahiyar Turai.
Matar, wadda aka kira ta da suna H.W, wadda ke zama a wani gari da ke kusa da birnin Paris na ƙasar Faransa, ta auri mijinta mai suna JC ne a shekarar 1984.
Sun haifi ‘ya’ya huɗu, ciki har da wata yarinya mai lalurar da ke neman kulawa a koda yaushe.
Auren nasu ya fara samun matsala ne a shekara ta 1992 lokacin da matar ta fara samun lalura.
Bayan shekara biyu, H.W ta daina kwanciyar aure da mijin nata, sannan a shekarar 2012 ta shigar da buƙatar neman raba auren, bayan mijin ya fara tsangwama da cin zarafinta.
A ranar Alhamis, kotun da ta yanke hukunci ta goyi bayan H.W, inda ta kafa hujja da cewa bai kamata a zargi matar da aikata wani laifi ba saboda kawai ta ƙi amincewa da mijin nata.
Shari’ar ta haifar da zazzafar muhawara kan ’yancin mata a cikin gidajen aure a Faransa.
