An harbe mutane yayin wani rusau a Kano

Spread the love

Mutum huɗu sun mutu a wani rikicin rusau a Rimin Auzinawa, Ƙaramar hukumar Ungogo, Jihar Kano, bayan da jami’an tsaro suka buɗe wuta kan masu bore. Rikicin ya samo asali ne sakamakon rusau da aka yi wa gine-ginen da aka kiyasta kusan 40, waɗanda ke gaban kammaluwa. Rahotanni sun bayyana cewa gine-ginen da aka rushe an ce suna kan filin da ke ƙarƙashin mallakar Jami’ar Bayero, Kano (BUK).

Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa ya ce hukumar KNUPDA ta taɓa tabbatar musu cewa filayen ba na BUK ba ne, amma daga bisani jami’an tsaro da ma’aikatan KNUPDA sun dawo da daddare suka rushe gine-ginen. Ya ƙara da cewa, yayin da mutanen yankin suka nuna rashin amincewarsu da rusau, jami’an tsaro sun buɗe wuta, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu da aka riga aka binne.

A halin yanzu, ƙoƙarin jin ta bakin hukumomi ya ci tura, yayin da ofisoshin KNUPDA ke cike da fargaba sakamakon tashin hankalin da lamarin ya haifar. Wani babban darakta a hukumar ya musanta cewa KNUPDA ce ta yi rusau, yana mai cewa kwamitin task force daga ma’aikatar ƙasa da tsare-tsaren birane ne suka aiwatar da aikin. Wani jami’i daga ma’aikatar ya tabbatar da cewa filin na Jami’ar BUK ne, inda ya ce gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba.

By ukarofi