
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar sojojin Nigeriya ta ce ƴan bindiga sun bai wa wani sarkin gargajiya Naira miliyan 1.5 don sayen filin da za su kafa sansani a yankin Amar na Jihar Taraba.
Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na riƙon ƙwarya a rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce sojoji sun tarwatsa wani sansanin ƴan bindiga a jihar tare da kashe ɗaya daga cikinsu da kuma ƙwato wani rumbun muggan makamai.
Ya ce lamarin ya auku ne a yankin Angwan Bala na Kambari Janar dake Ƙaramar Hukumar Karim Lamiɗo, a ranar Lahadi.
Jami’in ya ce a lokacin da aka samu bayanan sirri ne, sai jami’an suka gudanar da wani atisaye inda suka gano maɓoyar ƴan ta’addar.
A yayin haka ɗaya daga cikin ƴan ta’addan ya rasa ransa yayin da wasu guda 23 waɗanda daga cikin akwai mata 4 suka miƙa wuya.
Daga cikin makaman da aka ƙwato akwai bindigar AK47 guda 4 da mujallarsu guda biyar da kuma alburusan 7.62mm guda 80.
Sauran sun haɗa da ƙananun bindiga ƙirar ‘pistol’, da bindigun gargajiya da adduna 28, babura 16 da kuma barandami da wasu wuƙaƙe guda 48.
Kazalika, bincike ya nuna cewa asali ƴan bindigar daga jihar Filato suka yi ƙaura zuwa Taraba.
Kazalika ya jaddada cewa jami’an za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
