Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar Mai’adua Mamman Salisu Na Allah ya ce mutanen Nijar da Katsina uwa ɗaya uba ɗaya suke tun kaka da kakanni.
Na Allah yayi wannan magana ne a wata hira da manema labarai a ofishin sa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar ta Mai’adua.
Ya ce tun iyaye da kakanni akwai kyakkyawar haɗaka na aurataiyaa da kasuwanci a tsakaninsu wanda a yanzu ma ya haɓaka.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa dubban mutane daga Katsina da wasu sassan Arewacin ƙasar nan na shiga ƙasar Nijar,suma yan ƙasar Nijar suna shigowa Nijeriya harkokin kasuwanci da zumunci.
Ya kuma yi bayani mai tsawo akan irin aikace-aikacen da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar a ƙaramar hukumar waɗanda sauran ƙananan hukumomin jihar suma suka amfana.
Na Allah ya sanar da cewa daga lokacin da ya hau kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Mai’adua zuwa yanzu ya kashe fiye da Naira biliyan ɗaya wajen aiwatar da ayyuka daban-daban a yankin.
“Sun kuwa haɗa da gyaran makarantu da gina da gyara ƙananan asibitoci, gina hanyoyin musamman a karkara da aurar da zawarawa”inji Na Allah.
“Haka kuma ƙaramar hukumar ta ɗauki nauyin koyawa mata 1500 sana’o’in hannu tare da basu jari domin su tsaya da ƙafafun su”inji shugaban ƙaramar hukumar.
