Gwamnatin sojin Nijar ta kori ƙungiyar agaji ta Red Cross daga ƙasar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke duk wata yarjejeniya tsakanin ƙasar da ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross

Hukumomin sun kuma rufe ofisoshin ƙungiyar a faɗin ƙasar da kuma korar duk ma’aikatan ƙungiyar da ba ‘yan ƙasar ba.

Duk da dai ba a san dalilin yin hakan ba zuwa yanzu, an jima ana samun rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu tun watan Nuwamban bara, lokacin da ‘hukumomin Nijar suka nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da tallafin jin-ƙai da Tarayyar Turai take bai wa ƙungiyoyin masu zaman kansu, ciki har da Red Cross.’

Hukumomin sojin ƙasar sun furta cewa ƙungiyoyin ba su gudanar da ayyukansu a cikin hanyoyin da suka dace kamar yadda dokoki da yarjeniyoyi suka tanada ta hanyoyin hulɗa ta ƙasa da ƙasa.

Red Cross (Croiɗ Rouge) ta kasance a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar tun shekara ta 1990, inda kuma ta ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukanta a cikin ƙasar daga shekara ta 2007.

A lokacin da ƙungiyar ‘yan tawaye ta MNJ ta fara gudanar da ayyukan tayar da ƙayar baya a cikin ƙasar ta Jamhuriyar Nijar, ƙungiyar ta cigaba da taimaka wa al’ummar da suka tsere daga gidajensu ta hanyar samar masu da ruwan sha da sauran buƙatu.

A watan Nuwamba hukumomin sojin ƙasar sun dakatar da ƙungiyoyi biyu masu zaman kansu ba tare da sanar a hukumance ba hujojin da suka kawo ga hakan.

ƙungiyoyin sun haɗa da ACTED Agency for Assistance for Cooperation and Deɓelopment ko kuma Agence da la coperation pour l’assistance au Deɓeloppement da kuma APBE.

By ukarofi