Zamanantar da Kasuwar Rano zai jefa mu cikin mawuyacin hali – ‘Yan kasuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

‘Yan kasuwar babbar kasuwar garin Rano sun nuna matuƙar damuwarsu akan matakin da shugaban ƙaramar hukumar ke shirin aiwatarwa na rushe ta gaba ɗaya a sake mata sabon gini da suke fargabar hakan zai mutuƙar jefa su a cikin matsala.

Majiya mai tushe ta shaida mana cewa shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon. Naziru Ya’u ne ya nemi ‘yan kasuwar su tashi domin ya gayyato wani kamfani zai yi wa kasuwar gini na zamani sannan a sayarwa ‘yan kasuwa rumfunan.

Hakan tasa mazauna kasuwar da ta kafu kusan shekaru 100 suke gudanar da harkokin  kasuwarnci a  ciki hankalinsu ya tashi domin mafi yawa ba za su iya sake mallakar wajen ba idan an gina.

‘Yan kasuwar sun kai kokensu ga shugaban ƙaramar hukumar Nasiru Ya’u amma ya ce babu gudu babu ja da baya a shirinsa na rushe kasuwar da gina ta, don haka ma ‘yan kasuwar suka kai koke ga Sarkin Rano da sauran masu ruwa da tsaki a yankin akan a ja hankalin shugaban  domin kar ya jefa ‘yan kasuwar a yanayi mara daɗi amma ya kafe akai.

‘Yan kasuwar sun yi nuni da cewa gina irin wannnan kasuwar ko a cikin Birni ba kowa ne yake da ƙarfin mallakar tun da bare a karkara da ɗan kasuwa yake ɗan juya jarinsa ka zo ka karɓe musu rumfuna ka gina asa miliyoyin kuɗi da ba za su iya saya ba in an duba kashe-kashe sana’arsu basu kai ƙiyasin da za su iya sayen rumfunan ba sannan waɗanda suke da rumfunan tun na gado bana gwamnati ba, ba su da kuɗin da za su iya mallaka.

Mun tuntuɓi shugaban kasuwar Alhaji Alkasim Hamza ya tabbatar mana da cewa tabbas shugaban ƙaramar hukumar Nasiru Ya’u ya ce babu gudu babu ja da baya a wannan manufa tasa ta rushe kasuwar da tun iyaye da kakanni suke a wajen yace hatta wanda yake cikin rumfar Gwamnati ba za a biya shi diyya in an rushe ma saya za a sake yi idan an gina.

Ya ce sun kokawa shugaban ƙaramar hukumar ta gaba da gaba da ta rubuta masa takardu har ya kirawo wakilan ‘yan kasuwar ya zauna dasu a gaban DSS amma daga baya yace babu wanda ya isa ya hana shi ya rushe.

Alhaji Alkasim Hamza  shugaban Babbar Kasuwar Rano a madadin yan kasuwar sun yi kira ga Gwamnan jihar Kano jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a tausayi sa da adalcinsa ya sa  musu baki a wannan lamari kar  a tashe su  daga inda suka gada iyaye da kakanni suke kasuwanci.

Domin mafi yawan ‘yan kasuwar ba za su iya mallakar wajen ba, idan an gina suna ganin zai fi dacewa shugaban ƙaramar hukumar ya nemi wani filin na daban ya gina sabuwar kasuwa na zamani mai iko da halin saye sai ya saya.

Alhaji Alkasim Hamza Rano, ya ce ba suna jayayya ga shugaban ƙaramar hukumar ba ne, suna dai kira gare shi ne a yi musu adalci a yi la’akari da yanayi da halin da ake a ciki a tausaya musu kar a jefa su a halin rashin jin daɗi. Duk ƙoƙarin ji daga bakin shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon. Naziru Ya’u da wakilinmu ya yi akan lamarin ya ci tura

By ukarofi