Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse
Ministan tsaron Nijeriya Alh. Muhammad Badaru Abubakar (Mon, mni) ya ziyarci tsohon kwamishinan muhalli Hon. Ibrahim Baba Chai-chai a gidansa da ke unguwar Hausawa a birnin Kano.
Ministan ya ziyarci tsohon kwamishinan ne domin jajantamar akan rashin lafiya da yake fama da ita.
Badaru yayi addu’ar neman lafiya da ƙwarin jiki ga tsohon kwamashinan na Jihar Jigawa Alh Baba Chai-chai Allah ya bashi lafiya ameen.
Mataimakin gwamnan Jihar Jigawa Engr. Aminu Usman Gumel, shugaban jam’iyyar Apc na Jihar Jigawa Hon. Aminu Sani Gumel, sakataren kuɗi na jam’iyyar Apc na ƙasa Hon. Bashir Gumel, shugaban rukunin kamfanin Gerawa Alh. Isah Gerawa, Alh. Lawan Ya’u Roni, ƴan majalissun tarayya, ƴan majalissun dokokin Jihar Jigawa, tsaffin shugabannin ƙananan hukumomi da sauran ƴaƴan jam’iyyar APC ne suka rufawa ministan baya a yayin ziyarar.
A jawabin sa Hon. Ibrahim Baba Chai-chai yayi godiya da karamcin da ya samu ya ƙara da cewa hakan yana tabbatar da zumunci da riƙon amana a tsakaninsu da ministan da dukkan ƴan siyasa dake jihar ta Jigawa .
Sai dai bayan sauraran dukkan ɓangarorin biyu, ministan ya sami ganawa da Alh Ibrahim Baba Chai-Chai ta sirri wadda babu wani ɗan jarida da zai iya bayyana abinda suka tattauna.
Yayin da wasu suke tunanin wataƙila hakan bazai rasa nasaba da wasu ƙulle ƙulle irin na siyasa ba kasancewar yanzu harkokin siyasa sun fara kankama domin tinkarar zaɓen 2027 domin ganin jam,iyar APC bata sami wata matsala ba a dukkan matakin da ya kamata ace jam’iyyar ta kai bantenta.
