Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Cigaban da ake samu a harkar sadarwa da yaɗa bayanai ya kawo sauye-sauye da dama da za mu iya cewa sun amfanar da rayuwar ɗan adam wajen sauƙaƙa mu’amalarsa da harkokinsa na yau da kullum. Ba ma kawai abin da ya shafi isar da saƙonni da harkokin kasuwanci ba, har ma da batun ilimi da shugabanci, hatta a fagen addini da zamantakewa. Babu wani ɓangare na rayuwar ɗan adam da ba za ka samu bayanai a kansa ba, a yanar gizo ko zaurukan sada zumunta ba.
Sai dai duk da waɗannan nasarori da cigaba da aka samu, akwai wasu abubuwa da ɓatagari ke amfani da su ta hanyoyin da ba su kamata ba, domin karkatar da tunanin mutane daga gaskiya, yaɗa labaran ƙarya, ko rubuce-rubuce na ɓatanci da tunzura mutane, domin haifar da saɓani da rashin jituwa a tsakanin al’umma. Hatta mutane masu son zuciya da ’yan ta’adda marasa son zaman lafiya na amfani da shafukan su a zaurukan sada zumunta wajen cutar da mutane, ta hanyar damfara, sata, ko ɗaukar bayanan mutane da nufin cutarwa, da kuma karkatar da tunanin mutane zuwa ga wani tunani da bai kamata ba.
A makon da ya gabata wani rubutu da aka yaɗa shi a zaurukan sada zumunta ya tayar da hankalin jama’a da shugabanni a garin Jos, da ke tsakiyar Nijeriya, inda a shekarun baya aka yi ta samun tashe-tashen hankula da rikice-rikice masu nasaba da addini da siyasa. A sakamakon haka rayuka da dukiyoyi da dama sun salwanta, harkokin kasuwanci da zamantakewa sun gurgunce bakiɗaya. Kimanin shekaru 20 bayan abubuwan da suka faru a baya, sannu a hankali an samu dawowar zaman lafiya da mu’amala da juna. Amma a ýan kwanakin nan irin rubuce-rubucen da suke bayyana a zaurukan sada zumunta na nuna alamun da sauran Rina a kaba.
Rubutun da na samu damar karantawa wanda ya tayar da wannan ƙura ya fito ne daga wajen wani da ya kira kansa da sunan John Apollos Maton, wanda ya nuna cewa shi lauya ne. A cikin rubutun da ya yi wa taken, ‘ƙorafi kan amfani da amsa-kuwwa a masallatai: karya doka, tauye haƙƙoƙi da ƙuntatawa jama’a. A cikin rubutun da ya yi ya bayyana buƙatar a dakatar da amfani da amsa-kuwwa wajen kiran Sallah da Musulmi ke yi a masallatai, wanda a cewarsa yana takurawa jama’a da nuna fifikon wani addini kan wasu da kuma haifar da hayaniya a cikin jama’a.
Babu shakka wannan rubutu ya yi matuƙar ɗaga hankalin Musulmi da ke Jihar Filato, waɗanda ke ganin rubutun a matsayin wata hanya ta neman tsokana da tayar da zaune tsaye, wanda kuma babu abin da zai haifar sai fitina da zaman ɗarɗar a jihar. A matsayin martani da raddi daga ɓangaren al’ummar Musulmi, su ma sun yi rubuce-rubuce da ke sukar abin da wancan mutumin da ya kira kansa da lauya ya yi, suna masu bayyana shi da sunan jahili wanda bai san doka ba, kuma bai da wayewa kan addini da rayuwa, duk da karatun da ya ce ya yi a ciki da wajen Nijeriya.
Wani ƙarin abin damuwa kuma shi ne bayan yaɗuwar wancan rubutu, sai ga wasu baragurbin matasa ’yan soshiyal midiya da ke kiran kansu da ’yan jarida, suka fitar da wani rahoto dake cewa, wai gwamnatin Jihar Filato za ta hana kiran sallah da amsa-kuwwa. Ba tare da bincike don tabbatar da sahihancin wannan bayani ba, sai aka samu wasu ’yan taya ɓera ɓari suka fara yayata cewa, ai gashi nan ma har gwamnati ta fara yunƙurin kafa dokar hana amfani da amsa-kuwwa wajen ayyukan ibada.
Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa, nan da nan na kusa da gwamnati da suka san wannan bayani ba gaskiya ba ne, suka fitar da nasu rubutun da yake ƙaryata wancan soki-burutsun, domin kaucewa yaɗuwar jita-jitar da za ta iya haifar da wata fitina da ba a san inda za ta tsaya ba. Wannan abin a yaba ne, kuma yadda ya dace kenan a yi gaggawar ƙaryata jita-jita, a kuma ɗauki matakin da ya dace na hukunta waɗanda suka haifar da ita.
Kawo lokacin rubuta wannan sharhi Rundunar ’yan sanda ta Jihar Filato da Gwamnatin Jihar Filato ba su fitar da wani gargaɗi ko bayanai game da batun ba. Amma lallai akwai buƙatar jan hankalin jama’a musamman matasa masu amfani da zaurukan sada zumunta da su riƙa kiyayewa da abubuwan da suke yaɗawa a shafukansu, wanda zai iya haifar da tashin hankali da ƙalubalen tsaro, ba tare da sun kula ba.
Sai dai a wani faifan bidiyo da aka fitar, an nuna Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Isma’ila Adam yana ƙaryata wannan jita-jita da ake yaɗawa, inda ya ce babu wani abu mai kama da haka daga ɓangaren Gwamnatin Jihar Filato. Domin kuwa Gwamnan jihar Caleb Mutfwang duk abin da zai yi da ya shafi batun addini ko al’umma sai ya yi shawara da su, kuma idan sun bashi shawara yana ɗauka. Sannan ba ya goyon bayan duk wani abu da zai kawo fitina da rashin zaman lafiya. Wannan ya taimaka wajen kawar da wasi-wasin da ake ƙorafi akai a cikin Jos da Jihar Filato bakiɗaya.
Bayan fitar wannan bidiyo, wasu manema labarai sun rutsa Gwamna Mutfwang a wajen wani taro da ya je, inda suka nemi ƙarin bayani daga wajensa. A nan ne ya fito ƙarara ya nuna ba shi da masaniya kan wannan jita-jita, kodayake ya ji abin da ake faɗa kuma ya sa a yi bincike a kai. Amma ya buƙaci al’ummar musulmin Filato su yi watsi da wannan jita-jitar, don ba abu ne da hankali zai ɗauka ba, kuma shi ma ya yi tir da masu shirya irin waɗannan maganganu don a samu saɓani tsakanin Musulmi da Kirista a jihar.
Lallai akwai buƙatar gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da sun nemo wancan mutumin da ya fara yin rubutun da farko, a bincike shi don jin abin da ya sa ya yi wannan rubutu ya yaɗa shi a kafafen sadarwa ba tare da bin tsarin da ya kamata ba, a matsayinsa na lauya. Barin mutane suna yaɗa duk abin da suka ga dama, yana da haɗari, saboda halayyar mutane ta bambanta.
Gwamnati ta daina yin shiru akan irin waɗannan batutuwa da suka shafi tsaro da zaman lafiya. Kuma a riƙa gaggawar ɗaukar mataki, saboda kame baki ko kawar da kai, don a nuna abin shirme ne, wato irin abin nan da ake cewa, sai an kula kashi yake ɗoyi. To, wannan kashin rashin kula shi ne yake sa warinsa ya gallabi jama’a.
