Rundunar soja ta bayyana lambobin wayar masu kiran kansu shugaban sojin ƙasa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta samu ƙorafe-ƙorafe masu yawa dangane da wasu mutane da ke amfani da sunan Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, domin damfarar jama’a a shafukan sada zumunta.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na sojojin Nijeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar, ya bayyana cewa waɗannan ‘yan damfara na amfani da hoton janar ɗin a matsayin hoton bayanansu a shafukan sada zumunta domin aikata miyagun ayyuka. Har ila yau, suna shirya tarurrukan bogi ta yanar gizo a Zoom, WhatsApp, da Facebook, inda suke buƙatar mahalarta su tura wasu lambobi da ke bayyana a allon su, kafin daga bisani su shiga tattaunawa da su, su kuma damfare su.

Sanarwar ta kuma bayyana jerin lambobin wayar da waɗannan ‘yan damfara ke amfani da su, tare da yin kira ga jama’a da su guji duk wani taron intanet da ke amfani da hoton Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa a matsayin hoton bayanan shafi. Rundunar sojojin ta bukaci jama’a da su yi taka tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu mai kama da damfara ta hanyar kiran lambar 193, wacce ke aiki kyauta don ɗaukar matakin da ya dace.

Ga lambobin kamar haka : 09033949238, 09075323836, 09074272745, 08169257155, 08064561495, 08054138812,
09161521558, 09026515718,
09020898622, 08131333263,
09077188584, 08084529752, 08147409236, 09136497898, 09024627712, 07010119398, 09138997224, 09061549129, 08163593764 ,07035272009, 09018150412, 08093524443
Da 08088120581

By ukarofi