
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar (SSG).
Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya faɗi hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce naɗin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu.
Ya ce an naɗa Ibrahim ne sakamakon gogewa da ƙwarewarsa ta fuskar jagoranci wanda ake fatan hakan zai taimaka wajen haɓaka ayyukan ci-gaba a jihar.
Sabon SSGn ya kasance ma’aikacin gwamnati daga shekarar 1987 zuwa 2023 inda ya riƙe muƙamai a mataki daban-daban wanda hakan ya taimaka wa shugabanci a jihar.
Daga shekarar 2001 zuwa 2015 ne ya riƙe muƙamin babban sakataren ofishin bincike da harkokin siyasa a ƙarƙarshin ofishin SSG.
Haka kuma ya taimaka wa kawo sauyi da samar da ci-gaba a harkokin ilimi da na addini a jihar a lokacin da ya ke aiki, da haɗin-gwiwar Hukumar Ilimin Al’umma.
Kazalika, ya riƙe muƙamin sakatare a manyan kwamitoci a jihar inda ake fatan ya yi amfani da gogewarsa wajen tafiyar da sabon muƙamin nasa cikin ƙwarewa gami da taimaka wa ci-gaba.
Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa ga naɗa shi a matsayin sakataren wanda hakan zai taimaka wa ayyukansu na ci-gaba a jihar.
