Mun kashe mataimakan Bello Turji – Babban Hafsan Tsaron Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ce dakarunsu sun yi nasarar hallaka manyan kwamandojin sansanin jagoran ƴan bindiga, Bello Turji.

Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin hafsoshin tsaro na haɗaka a Abuja, ranar Juma’a.

Ya ce wasu daga cikin kwamandojin da aka kashe yayin wani atisaye a ranar Alhamis, sun haɗa da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.

Nasarorin da sojoji suke samu akan ƴan bindiga a Zamfara sun sanya Turji shiga halin rikicewa tare da guje wa kamun dakarun a ƙoƙarinsa na tserewa, kamar yadda CDS ɗin ya bayyana.

Haka kuma, ƙara kutsawa cikin ƙauyuka da jami’an ke yi da tarwatsa dabobin ƴan bindigar na tilasta musu shiga ƙungurmin daji.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun aika da saƙo mai ƙarfi ga baki ɗaya ɓangarorin ƴan ta’adda na cewa ƙarshen ta’addanci ya zo a Nijeriya.

Kazalika, ya tabbatar da cewa rundunar soji za ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta shafe dukkanin ayyukan ta’addanci a Nijeriya ta yadda rayuka da dukiyoyin al’umma za su samu cikakken tsaro.

By Babaji