Gwamnatin Katsina ta tallafa wa manoma da garmar shanu 4000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarin da take na sauƙaƙa wa manoma tare da bunƙasa noman rani gwamnatin Dikko Raɗɗa ta tallafawa kananan hukumomi 34 ad garmunan shanu guda 4000.

Garmunan da ta saya akan Naira biliyan dubu huɗu an baiwa kowacce ƙaramar hukuma guda 100.

Gwamnatin jihar ta sayi Kowane ɗaya akan Naira miliyan ɗaya amma saboda kudirin sa na sauƙaƙawa manoma yasa aka sai da masu akan Naira dubu ɗari da hamsin.

Shugaban ƙaramar hukumar Abdullahi Sani Safana ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a ofishin sa.

Ya bayyana wasu ƙoƙarin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta yi a fannin noma da suka haɗa da bada iri kyauta da takin zamani da aka raba wa manoma kyauta a duk ƙananan hukumomi kyauta.

“Akan harkar tsaro kuwa shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauka ya taka rawa wajen kawo zaman lafiya a ƙaramar hukumar”inji Sani Safana

Dama gwamna Raɗɗa yayi alƙawari da yaci zaɓe an rantsar da shi matsalar tsaro zai fara tunkara.

“Ya samar mana da motoci na Sulke guda biyu tare da kawo jami’an tsaro na al’umma CWC da sojoji tare da sauran jami’an tsaro da a kullum suna zirga zirga ba dare ba rana domin tabbatar da tsaro a yankin”shugaban ƙaramar hukumar ya ce.

Safana ya bayyana ƙaramar hukuma Safana cewa ita ma tana cikin shirin hukumar UNDP na gina wa yan gudun hijira gidaje guda 150 a yankin.

Ƙaramar hukumar safana na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan ta’adda suka ɗaiɗaice inda harkokin noma, ilimi, kasuwanci da kiwon lafiya ya taɓarɓare a yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana wasu aikace-aikace na raya ƙasa da suka gudanar da ya haɗa da gina magudanan ruwa a faɗin ƙaramar hukumar.

Gyaran fanfunan tuƙa tuƙa da gina wasu, da gina azuzuwa a makarantun firamare da gyara asibitoci da sauran su.