Akwai wasu zaratan ‘yan ƙwallo da asalinsu ‘yan Nijeriya ne, amma suke wakiltar wasu ƙasashen duniya.
Wasu zaratan ‘yan ƙwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, waɗanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu bakiɗaya ko wani ɓangare daga cikin iyayen nasu ’yan Nijeriya ne.
Na farko shi ne – Jamal Musiala:
Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen ɗan ƙwallon ƙasar Jamus ne da ƙungiyar Bayern Munich ta Jamus ɗin kuma yana cikin matasan ‘yan ƙwallon da suke tashe a duniya a yanzu.
An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin ɗan Nijeriya ne, wanda ya yake da shaidar zama ɗan Ingila, mahaifiyarsa mai suna Carolina kuma ’yar Jamus ce.
Ya wakilci ƙasar Ingila a ƙwallon matakin yara, kafin ya koma Jamus da taka leda.
Ya lashe kofuna da dama irin su gasar Bundesliga guda huɗu da sauran kofuna, sannan ya samu kyaututtuka da dama.
Karim Adeyemi:
Karim-David Adeyemi wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2002, ɗan wasan Jamus ne da ƙungiyar Dortmund.
An haifi ɗan wasan a birnin Munich, wanda mahaifinsa asalin ɗan Nijeriya, amma mahaifiyarsa ’yar Romaniya ce.
A kwanakin baya ɗan wasan da ke taka leda a Dortmund da ke Jamus. A baya-bayan nan Karim Adeyemi ya bɗɗe wata gidauniya a Nijeriya.
Ya buɗe gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke jiyar Oyo a kudu maso yammacin Nijeriya, inda ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi.
A lokacin da ya ziyarci Najieriya, Adeyemi ya shaida cewa nan gaba yana tunanin komawa taka leda a gasar firimiyar Ingila.
Michael Olise:
An haifi Michael Akpoɓie Olise, a ranar 12 ga Disamban 2001, ɗan ƙwallo da a yanzu yake wakiltar Faransa kuma yake taka leda a ƙungiyar Bayern Munich.
Asalin mahaifinsa ɗan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa ’yar Aljeriya ce mazauniyar Faransa.
Noni Madueke:
Asalin sunansa Chukwunonso Tristan “Noni” Madueke, kuma an haife shi ne a ranar 10 ga Maris a shekarar 2002.
Yanzu yana wakiltar ƙasar Ingila ne, sannan yana taka leda a ƙungiyar Chelsea ta Ingila.
Asalin mahaifinsa ɗan Nijeriya, amma shi a Ingila aka haife shi.
Bukayo Saka:
Bukayo Saka fitaccen ɗan ƙwallo ne da a yanzu yake jan zarensa a ƙungiyar Arsenal ta Ingila.
ɗan wasan wanda asalin sunansa Bukayo Ayoyinka Temidayo Saka, iyayensa Adenike da Yomi Saka duka ’yan Nijeriya ne.
Sai dai ya sha bayyana cewa yana alfahari da kasancewarsa ɗan Nijeriya, kuma yakan ziraci ƙasar.
Ethan Chidiebere Nwaneri:
Ethan Chidiebere Nwaneri wanda aka haifa a ranar 21 ga watan Maris na 2007, matashin ɗan wasa ne da a yanzu yake tashe a ƙungiyar Arsenal.
An haife shi ne a arewacin Landan, amma iyayensa ’yan Nijeriya.
Ya wakilta tawagar ’yan wasan ƙasa da shekara 16 da 17 da 19.
Har yanzu ba wakilci babbar tawagar Ingila ba, wanda hakan ya sa za a iya gayyatarsa Nijeriya.
Joshua Orobosa Zirkzee:
Joshua Orobosa Zirkzee wanda aka haifa a ranar 22 ga Mayun 2001, ɗan ƙwallo ne da yake wakiltar ƙasar Netherlands, kuma yake taka leda a ƙungiyar Manchester United ta Ingila.
An haife shi ne a birnin Schiedam, sai dai shi mahaifiyarsa ce ’yar Nijeriya, amma mahaifinsa ɗan Netherland ne.
