Hukumar Gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta dakatar da mai horar da ‘yan wasanta, Usman Abdallah har tsawon makonni uku.
Sanarwar da shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, Alhaji Ali Muhammad Umar ya fitar, ta ce mataimakin mao horarwar, Ahamd Garba Yaro-Yaro ne zai ci gaba da riƙon muƙamin nasa.
Wannan ya biyo bayan rashin kataɓus ɗin da ƙungiyar ta yi a baya-bayan nan, haɗi da harzuƙa magoya bayan ƙungiyar, bayan tashi daga wasan da Kano Pillars din ta yi kunnen doki da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Yaro-Yaro zai ci gaba da horar da ‘yan wasan na Pillars, har sai kwamitin binciken da ƙungiyar ta kafa ya miƙa rahotonsa.
A makon jiya ne, Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Ikorodu City da ci 4-1, a birnin Legas.