Ba don rubutu ba da addini bai zo mana ba – Rahama Sabo Usman

Spread the love

“Mahaifiyata ce ta sa na fara rubutun littafi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Tauraruwar adabinmu ta wannan mako ba kowa ba ce face, Malama Rahama Sabo Usman, marubuciya daga Jihar Kano. Wacce ta yi fice a ýan shekarun baya, sakamakon gwagwarmaya da ta yi da yaɗuwar rubutun batsa, wanda har ya kai ga kafa wata babbar ƙungiya da aka yi wa rijista da sunan, Gamayyar ƙungiyoyin Marubutan Jihar Kano (GAMJIK). Rahama ta kasance marubuciya mai baiwa da yawa, bayan kasancewarta mai rubutun labaran hikayoyi da gajerun labarai, tana kuma rubutun wasan kwaikwayo, da ɗora murya a wasannin kwaikwayo na rediyo da talabijin. Harwayau kuma, tana taɓa rubutu da harshen Turanci. ɗaliba ce ta addini da boko, inda take da haddar Alƙur’ani da kuma digiri a ɓangaren ilimin halittu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana abin da ya zaburar da ita ga shiga harkar rubutu da burin da take da shi a kansa. Ga yadda hirar tasu ta kasance. 

MANHAJA: Ko za mu fara da sanin cikakken sunan marubuciyar? 

RAHAMA SABO: Cikakken sunana shi ne Rahama Sabo Usman, ni marubuciya ce kuma ɗaliba, daga Unguwar Kwana Huɗu da ke ƙarƙashin Gama C, a mazaɓar ƙaura Goje, cikin ƙaramar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano. Ni ce sakatariyar Gamayyar ƙungiyoyin Marubutan Jihar Kano ta GAMJIK ta farko. Ni budurwa ce, ban taɓa aure ba, sai dai ina sa ran yi a nan gaba. 

Za mu so mu san wani abu daga tarihin rayuwarki?

Kamar yadda na faɗa a farko ni haifaffiyar Jihar Kano ce daga ƙaramar Hukumar Nasarawa. Na halarci makarantar firamare a Unguwar Gama, na kuma yi sakandiren ‘yan mata ta Dabo da ke kan titin France a Unguwar Sabon Gari a yankin ƙaramar Hukumar Fagge.

Bayan na kammala ne sai na halarci makarantar share fagen shiga jami’a ta CAS, kafin na ƙara samun tagomashin ƙara faɗaɗa karatuna zuwa Jami’ar Bayero, na samu shaidar digirina na farko a ɓangaren koyar da ilimin kimiyyar halittu masu rai wato Biology. 

A ɓangaren ilimin addini kuwa, na yi karatun sanin baƙin Alkur’ani har zuwa ga sauke shi a wurin mahaifiyata. Daga nan na shiga Madarasatul Markazul ƙur’an, inda na fara ƙoƙarin haddar Alƙur’ani har zuwa lokacin da na samu ijaza ta hattama haddar Alkur’ani mai girma. Na karanci littattafai da dama na addini waɗansu a wurin mahaifiyata, waɗansu a wurin wasu malaman daban. Na yi karatun Kutubu Sitta, a wurin Malam Aminu Ibrahim Daurawa, na yi karatun littafin Ahkamul Jana’iz a wurin Imamu Ahlussunnah Sheikh Abdulwahab Abdallah. Wannan shi ne tarihina a taƙaice. 

Yaushe kika fara rubutu kuma mene ne silar fara rubutun?

Na fara rubutu a shekarar 2016, sai dai ban zama cikakkiyar marubuciya a lokacin ba. 

Tun daga sannan ban ƙara ɗora alƙalami a kan tawada ba har zuwa farkon shekarar 2020. A nan ne na shigo duniyar marubuta tsundum, har Allah Ya nufa na zo inda nake a halin yanzu.

Dalilin fara rubutuna kuwa ba ya rasa nasaba da tursasawar mahaifiyarta, da take jin cewa zan iya, duk da ni a lokacin ina ganin cewar ba zan iya ɗin ba.

Dalilinta na tursasa min kuwa shi ne, ta san cewa ni cikakkiyar makaranciya ce da ke da naci da bibiyar karatun Hausa tun ina da shekara takwas. Tun tana duka da zagi (domin tana ganin ƙarancin shekaruna), har ta kai taƙin da ta haƙura ta bar ni a salon soja malamin kansa. Ita ce ta tursasa ni na fara rubutu, yayin da ta ji sanarwar BBC Hausa sun buɗe gasar mata zalla ta Hikayata. Tun a shekarar farko da suka fara take ƙoƙarin ganin na shiga ina kaucewa. A ganina ni ba marubuciya ba ce, kuma zan taɓa iya rubuta ba. Ita kuma hangenta, yanzu ya kamata in amfani karatun littattafan da na dinga yi a baya.

Ganin haƙonta bai kai ga nasara ba, ta haƙura a shekarar. Wata shekarar tana zagayowa ta rantse sai na shiga, don a lokacin ma ba ni da babbar waya, ita ta ba ni kuɗi na sayo littafi da biro, ta hana ni yin komai a gida, ta ce in shiga ɗaki in kulle kaina, in yi tunanin labari mai ma’ana. 

Gudun ɓacin ranta ya saka na amsa buƙatarta, na shiga ɗaki na yi ta tunani, da ƙyar na samu na rubuta wani labari. Ina nuna wa yayana, ya tuntsire da dariya, ya yi ta nuna wa sauran ‘yan gidanmu ana ta dariya wai labarin bai yi ma’ana ba. Ita kuma baiwar Allah, har a lokacin ƙarfafa min gwiwa take yi, tana jin cewa zan iya. A haka dai na ƙara matsawa har sati biyu na rubuta wani labari a kan jigon fyaɗe. Idan ba zan mance ba wurin Malam Kabir Yusuf Anka na je, ya tace min rubutun ya mayar min da shi bugun yanar gizo (soft copy). Na tura labarin har kuma na samu damar shiga cikin mutane (25) da BBC Hausa ta duba labaransu a shekarar.

Shekara ta biyu kuma, ra’ayina ne ya kai ni. Bayan na kammala makarantar share fagen shiga jami’a (CAS) na zauna zaman jiran damar fara ɗaukar ɗalibai. Kafin na samu, na tutuɓi wata ƙawata da muka kammala karatun tare na ce mata ko za mu jarraba rubutun onlayin da ake yayi yanzu? Sai ta ce mini in jira har mu samu damar shiga jami’a. Daga nan ba mu ƙara maganar ba, har muka fara karatu. Ita ta riga ni fara rubutu, saboda na riga ta fara karatu, sai daga baya ta samu shiga ta tarad da mu.

Sai da muka kammala jarrabawar zangon farko sannan na fara nawa. Lokacin da na tura mata na ce ta duba ta ga ko ya yi, sai ta ce bari ta saka ni a guruf ɗin da za a duba mini, shi ne ta saka ni a guruf ɗin marubuta na First Class Writers Association. 

Yaya alaƙar ki take da marubuta da kuma makaranta?

Tsakanina da marubuta akwai soyayya da tarin girmamawa. Tsakanina da masu karantu kuwa sai hamdala. Wasu ma sun zama kamar ‘yan uwana na jini. 

Waɗanne hanyoyi kike bi wajen zaɓar jigo idan za ki yi rubutu?

Nakan zaɓi jigo ne a yadda rayuwa ta zo mini. Wani lokacin saboda abin da na ga yana faruwa, yake faruwa ko kuma ya faru a duniyar da ke kewaye da ni. Wani lokacin kuma ma abin da ya faru, yake faruwa a kaina nake rubutawa. 

Idan da za a ba ki damar kawo sauyi a wasu matsaloli da ke ci wa marubuta tuwo a ƙwarya da wacce matsala za ki fara?

Gaskiya da matsalar satar fasaha zan fara, domin a ganina ta fi kowacce matsala dawo da rubutu da marubuta baya.

Ya kike kallon rubutu a jiya da yau ta fuskar cigaba da koma baya?

Zan iya cewa marubuta sun samu gagarumin cigaba ta fannoni da dama, musamman zuwan rubutu a yanar gizo. Na farko a yanayin tsaftar muhalli an yi ƙoƙari matuƙa wurin mayar da muhalli ya zama cikin kintsattsen tsari da babu tarin takardu, sannan an rage kashe kuɗi, saboda littattafan da muke saka dubu ɗaya a yanzu za mu iya samun shi a arha ɓagas. Ni kaina da ba na iya tara ko sisi saboda tsabar sayen littafi, yanzu an hutar da mu zuwa kasuwa saya, ko kuma wurin masu bayar da haya. Harwayau, ya bai wa mutane da dama damar zama marubuta, ciki kuwa har da ni. ƙila da babu rubutun yanar gizo da ba zan taɓa zama marubuciya ba.

A dunƙule dai zan iya cewa zuwan rubutun yanar gizo shi ne babban cigaban da marubuta suka samu a wannan zamanin. Zan iya cewa kuma shi ne babban cibaya da harkar rubutu ta samu, musamman ta hanyar kashe adabin da ake wa laƙabi da Adabin Kasuwar Kano. Marubuta, masu sayar da littafi, masu bayar da haya, masu sayar da ƙosai ko nama (da ake bai wa takardu), masu buga littattafan, kai har da masu kwashe shara ma sun rasa gwaggwaɓan ciniki ta hanyar zuwan rubutun yanar gizo. 

Me za ki iya cewa game da tasirin marubuta a cikin al’umma?

Marubuta suna da matuƙar tasiri wurin gyaran al’umma, don zan iya cewa ba domin rubutu ba da addini bai zo mana ba. Alkur’ani rubuta shi aka yi, hadisi rubuta shi aka yi, dukkanin wani abu mai daraja da muke taƙama da shi rubuta shi ake yi.

Malaman Larabci suna cewa, duk abin da aka haddace zai gudu, amma abin da aka rubuta zai zauna muddin ba goge shi aka yi ba. Marubuta su ne suke rubuta abin da ake ƙaruwa da shi a addini. Marubuta suna gyara zamantakewar aure, suna gyara mu’amalar Rayuwa ta yau da Kullum. Suna kuma dakushe wata illa da suka hango. Zan iya cewa marubuta su ne ƙashin bayan ginin kowacce al’umma.

A wanne yanayi kika fi jin daɗin yin rubutu, kuma me ya sa?

Na fi jin daɗin rubutu, yayin da na toshe kunnena ina sauraron daddaɗan sautin Alƙur’ani mai girma. Dalilina kuwa shi ne, na fi shiga nishaɗi a irin wannan yanayin. Na fi jin babu kowa a duniya face ni kaɗai, kai a taƙaice na fi samun ilhamar yin rubutu a wannan yanayin. 

Duk wani abu na rayuwa tattare yake da ƙalubale da nasarori, ko za mu iya sanin wasu daga cikin nasarori da ƙalubale da suka shafi rubutunki?

Babbar nasarata a harkar rubutu ita ce, samun damar hulɗa da mutane mabambanta masu ra’ayoyi mabambanta, masu tarin ilimi da baiwa ta musamman. Zan iya cewa babu wani ƙalubalen rayuwa takamaimai da zan nuna wanda na samu sanadiyar rubutu. 

A cikin jerin marubutan online da masu bugawa su wane ne gwanayenki? Kuma ko akwai waɗanda kike kallo a matsayin allon kwaikwayo ko iyayen gida?

A wurina kowanne marubuci ɗanbaiwa ne, mai ƙwaƙwalwa ta musamman. Ba zan iya ware marubuci ko marubuciya guda ɗaya in ce ita ce allon kwaikwayona ba. Ina jinjina baiwa da fasahar marubuta, ina kallon kowanne marubuci a matsayin allon kwaikwayo. Ko miniti ɗaya na yi da marubuci ina ƙaruwa da shi ta fannoni da dama.

Kin taɓa shiga wata gasar marubuta, ko kin taɓa samun nasara?

Gaskiya ni ba gwanar shiga gasa ba ce. Amma ni a yadda na ɗauki lamarin gasa, duk gasar da na shiga na tsara labari na tura, sunanta wacce na yi nasara, domin sai na yi yaƙi da zuciyata na yi nasara kafin ta bar ni na shiga. Kuma ina ɗaukar duk wani rubutu da zan rubuta a matsayin nasarata. Duk da a nasarar ma akwai fitacciya kuma zaɓaɓɓiyar nasarar da ake fitar da zaƙaƙurai. A irin wannan ƙadamin dai gaskiya nasarar ba ta da wani yawa. Amma ba zan mance da nasarar da na samu a gasar da reshen ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Filato ya saka, inda har na samu nasarar zamowa ta ɗaya. Sai kuma gasar da zauren marubuta na WhatsApp suke shiryawa ita ma na taɓa zuwa ta ɗaya.

Kawo yanzu littattafai nawa kika rubuta, kuma shin akwai waɗanda kika buga ko duka a onlayin ne?

Na rubuta littattafai guda biyar da suka haɗa da ‘Ba Yin Kaina Ba Ne’, ‘Makauniyar Rayuwa’, ‘Soyayyata da Shi’, ‘Lauje Cikin Naɗi’, da kuma ‘Ina Matsalar Take?’. Amma guda ɗaya na samu damar bugawa shi ne, ‘Ina Matsalar Take?’. 

Shin kin taɓa yin wani rubutu da kika yi danasani a kansa?

Gaskiya ban taɓa yin wani labari da na taɓa yin danasani a kansa ba. 

Kina daga cikin marubutan da suka assasa Gamayyar Marubutan Jihar Kano (GAMJIK), kasancewar akwai ƙungiyoyi da yawa kafin ita, me ya ja hankalinku kuka ga dacewar samar da ƙungiyar?

Mun kafa ƙungiyar GAMJIK ne domin yaƙi da yawaitar rubutun batsa, da kuma yadda aka mayar da rubutun onlyin ya zama ta ci barkatai, babu tsari babu doka. Sannan muna ƙoƙarin samar da haɗin kai tsakanin marubuta da kuma samar da soyayya. GAMJIK ta kasance ƙungiyar marubutan onlayin ta farko da ta ci nasarar ƙulla ƙarfaffen zumuncin da ake haɗuwa akai-akai ana tattaunawar gani da ido. 

Wacce shawara za ki bai wa sababbin marubuta da masu sha’awar fara rubutu?

Shawarar da zan ba su ita ce, su kyautata niyyar da za ta kawo su duniyar rubutu. Su shigo duniyar rubutu da aniyar kawo gyara da cigaban al’umma. Kar su shigo duniyar rubutu da aniyar rubutu domin samun wani ɗan mata’i na duniya, ko kuma da niyyar rubuta wani abu da zai janyo ruguza rayuwa da tarbiyyar al’umma.

Zan kuma rufe da ba su shawarar da nake yawan bai wa marubuta. Su ji tsoron Allah, su tsarkake alƙalaminsu, su tuna a duk abin da ka aikata akwai tambaya ciki kuwa har da rubutu. Su tuna cewa akan alƙalami fa akwai tambaya, kar su rubuta abin da bayan sun mutu duk wanda ya karanta za a dinga tashin su ana yi musu azaba a kai.

Shin bayan rubutun zube kina taɓa rubutun wasan kwaikwayo? Idan haka ne wanne fim kika rubuta?

E, ina taɓa rubutun fim da na rediyo. Kamar a na fim na rubuta labarin ‘Kwaleji’, ‘So Jarabta’, ‘Matakin Nasara’, da sauran su.

A na rediyo kuma na rubuta wani labarin turanci mai taken, ‘Adɓenture of Wazobiya’. Sai kuma na yi rubutun sanin makama (internship) na wani labari mai suna, ‘Albishirin Ku’.

Wanne bambanci kike ganin akwai tsakanin marubutan onlayin da kuma masu talifin littattafansu? 

Haɗin kai. Wannan shi ne babban bambancin mu, ba wai don sun fi mu haɗin kai ba, sai don sun fi mu kusanci da juna kowa ya san kowa. Saɓanin mu da wani ma bai san da rayuwar wani ba.

Wanne abu ne ya fi saurin burge ki? Kuma wanne ya fi ba ki haushi?

Abin da ya fi birge ni shi ne a duniya in ga na aikata abin da mahaifiyata take so. Abin da kuma ya fi ba ni haushi shi ne, ina ga mutane suna aikata saɓon Allah muraran, kuma ba sa jin kunyar kowa. Ba kuma sa jin wa’azi ko ɗaukar shawara. 

Shin bayan rubutu akwai wata bai wa da kike da ita?  

Bayan rubutu na iya ɗora murya (Voice over). Ina karanta labarai masu sauti, da kuma fitowa a matsayin jaruma a wasannin kwaikwayo na rediyo. 

Zuwa yanzu menene babban burinki a harkar rubutu? 

Babban burina shi ne in ga na dage ina rubutu, gandar da nake samu a rubutu ta kau. Ina kuma da burin ganin na gama da rubutu lafiya, na rubuta abin da ko bayan ba ni da rai za a dinga yi mini addu’a.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki? 

Mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha romon sa!

By ukarofi