Gwamnatin Kano ta haɗa kai da dillalan filaye don bunƙasa tsaro da tattali

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi ganawa ta musamman da ƙungiyar dillalan filaye da ci-gaba don bunƙasa harkokin ɓangaren da nufin inganta tsaro da ci-gaban tattali a jihar.

Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma’aikatar, Sani Abba Yola ya faɗi hakan a yayin ganawar, inda ya ce kwamishinan ya jaddada rawar gani da dillalan za su taka wajen tabbatar da tsaro da harkar tattali a jihar.

Waiya ya koka ga yadda wasu ke sayen filaye ko su yi hayarsu don gudanar da haramtattun ayyuka acikinsu wanda hakan barazana ce ga zaman lafiyar al’umma.

Ya ce ma’aikatarsu tana aiki tuƙuru wajen ganin ta haɗa kai da ƙungiyoyin da kai tsaye ayyukansu ke isa ga al’umma, yana mai kira ga dillalan da su riƙa kiyaye ƙa’idodin da ɗoka da amince da su wajen harkokinsu.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Isa Jibrin Isa, ya jinjina wa Kwamishinan bisa inganta harkokin ofishinsa, ya na mai masa alƙawarin ba su cikakken goyon baya da tallafin da ake buƙata wajen cimma nasara.

Ya kuma koka ga yadda wasu ke shiga harkar dillanci ba tare da yin rajista da ƙungiyar ba wanda hakan ya kan haifar da koma baya, ya na mai kira ga gwamnati da ta samar da tsare-tsare da za su bunƙasa hanyoyin dillanci a jihar.

By Babaji