
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada aniyarta ta cigaba da kula da yara da inganta rayukansu ta hanyar samar da shirye-shirye da za su bada damar samun ilimi da kiwon lafiya da walwalarsu acikin al’umma.
A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na musamman, Sani Abba Yola na Ma’aikatar Labarai da Harkokin Cikin gida ya fitar, Kwamishina, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan ne a yayin taron inganta al’umma da aka yi wa ɗalibai a Jami’ar Bayero da ma’aikatar ta shirya da haɗin-gwiwar Asusun Kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF.
Ya ce a ƙoƙarinsu na bunƙasa ilimin ƴaƴa mata, sun bai wa ɗalibai mata kuɗaɗe daga N20,000 zuwa N70,000 don rage masu halin matsin yanayin karatu.
Haka kuma an buɗe makarantun kwana na mata da aka rufe su a baya, waɗanda a yanzu haka ana gudanar da harkokin karatu cikin lumana.
Kwamishina Waiya ya ƙara da cewa, gwamnati ta kuma saya da gyara motocin ɗaukar ɗalibai mata don sauƙaƙe masu hanyoyin ɗaukar karatukansu.
Bugu da ƙari, kimanin ɗaliban makarantun firamare 700,000 ne suka samu kayan makaranta (inifom) a kyauta daga gwamnati, ƙoƙarinta na bai wa harkar iliminsu muhimmanci.
