
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan wasa Jude Bellingham ne ya zura ƙwallon da ya bai wa Real Madrid nasara inda ta doke Manchester City da ci 3 da 2 a wasan farko na gasar Zakarun Nahiyar Turai a rukunin ƙalubale.
Erling Haaland shi ya fara zura ƙwallo biyu a ragar Madrid wanda ɗaya ya samu ne a bugu fenareti, inda daga bisani Kylian Mbappe ya farke ɗaya a minti na 60.
Ana tsaka da haka ne tsohon ɗan wasan City, Brahim Diaz ya ƙara ta biyu a ragar Manchester wanda hakan ya mayar da wasan kunnen doki, kana daga bisani Bellingham ya zura ƙwallon da ta bai wa Madrid nasara a mintinan ƙarshe.
A yanzu haka dai Madrid ta samu dama akan takwararta na kai wa zangon ƙungiyoyi 16 a yayin ake jiran karawa ta biyu a filin wasa na Bernabeu dake ƙasar Sifaniya.
