
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi ganawa ta musamman da ƙungiyar dillalan filaye da ci-gaba don bunƙasa harkokin ɓangaren a harkar dillanci da inganta tsaro da harkokin tattali.
A lokacin da ya ke magama, Kwamishina Waiya ya ce akwai buƙatar samar da dokokin da za su daƙile ayyukan sata da ake yawan samu sakamakon rashin bin ƙa’idodin cinikayyar filaye.
Ya koka kan yadda wasu ke sayar ko hayar fili da gudanar da haramtattun ayyuka acikinsu, ya na mai cewa lallai ne a yi nazari game da tasirin hakan acikin al’umma kuma a ɗauki matakin dakatarwa.
Ya ce lallai sai dalillai sun kiyaye sharuɗɗa da doka ta tanadar wajen tabbatar da tsaro, ya na mai nuna muhimmancin haɗa kai da ƙungiyoyi da ma’aikatarsa ta ke yi don maslahar al’umma.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Isa Jibrin Isa, ya jinjina wa Kwamishinan bisa inganta harkokin ofishinsa, ya na mai masa alƙawarin ba su cikakken goyon baya da tallafin da ake buƙata wajen cimma nasara.
Ya kuma koka ga yadda wasu ke shiga harkar dillanci ba tare da yin rajista da ƙungiyar ba wanda hakan ya kan haifar da koma baya, ya na mai kira ga gwamnati da ta samar da tsare-tsare da za su bunƙasa hanyoyin dillanci a jihar.
