Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dakarun Operation Fansan Yamma sun daƙile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto inda aka kashe ‘yan ta’adda da dama.
Mai magana da yawun rundunar ta Operation Fansan Yamma, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau Laraba a Gusau babban birnin jihar.
A cewarsa, an gudanar da aikin ne tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.
“Wannan farmakin ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama da suka haɗa da wasu manyan jagororin su, don tabbatar da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin alummar jihohin biyu”. Ya ƙara da cewa
Ya Kuma bayyana cewar, a lokacin, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama da suka haɗa da shugabannin su irin su Kachalla Na Faransa, Dogon Bakkwalo, Auta Gobaje da Ɗan Mai Dutsi da dai sauransu.
“Musamman, an kawar da da yawa daga cikin waɗannan mutane a wani ƙazamin faɗa da aka yi a ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi (LGA) na Jihar Zamfara da kuma ƙaramar hukumar Isa ta Jihar Sokoto”.
Laftanal Kanal Abubakar ya kuma ƙara da cewa, ayyukan sun kuma wargaza ƙungiyar ta’addanci tare da lalata hanyoyin tallafa musu, tare da raunana ƙarfin su.
A cewarsa, an yi kiyasin an lalata sansanonin su guda 40 a lokacin farmakin .
“Wannan gagarumin farmakin na da matuƙar muhimmanci wajen kawo cikas ga dabarun ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma”. Ya ƙara da cewa
Laftanar Kanar Abubakar ya yi nuni da cewa, sojojin sun ƙwato tarin makamai da alburusai, wanda zai zama muhimmi wajen hana kai hare-hare a tsakanin ‘yan’taaddan a nan gaba.
Ya ci gaba da cewa sojojin sun kuɓutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su a yayin farmakin, wanda hakan ya taimaka wajen samar da tsaro da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
A cewar sa, rundunar ta Operation Fansan Yamma tana cigaba da jajircewa wajen kawo cikas ga ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai kan ‘yan ta’addan da suka gudu har da Bello Turji da muƙarrabansa ga hukumar tsaro don samun nasarar kakkaɓe su.
“Rundunar Operation Fansan Yamma ta kuma tabbatar wa da alummar yankin cewa zasu samu kariya da gudunmawar da suke bayarwa cikin sirri da mutuntawa”. In ji Laftanar kanar Abubakar
