Gwamnatin Kano ta yi tir da shirin APC na kafa gwamnati cikin gwamnati a jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A kwanan ne aka samu wasu kalamai da aka jingina su ga Shugaban masu kishin jami’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Usman Alhaji, na sanar da cewa za su kafa ɓoyayyar gwamnati a Jihar Kano, wanda ba iya lamarin siyasa ba, har ma ka iya zama haɗari ga jihar da ma demokraɗiyya a ƙasa bakiɗaya.

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, inda ya ce a tsarin da Nijeriya ke tafiya a kai ta demokraɗiyya, haramun ne kafa wata gwamnati a da’irar wata gwamanti.

Ya ce, kasancewar dokar ƙasa ta bada damar faɗar albarkacin baki, ba daidai bane kuma mutum ya faɗi abinda ya ga dama ba tare da la’akari da hukuncin doka akan hakan ba.

Waiya ya bayyana hakan a matsayin wani salo da jam’iyyar adawa ta APC ta ɗauka wajen haddasa tashin-tashina a jihar, wanda kuma gwamnati ba za ta lamunta ba.

Ya kuma ce mutanen kirki na jihar su suka zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda a cikin ƙaramin lokaci ya cimma nasarori da dama.

Kwamishina Waiya ya kuma ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ita ce wadda ta fi kowacce gwamanti a Nijeriya wajen cimma manyam manufofin buƙatun rayuwa, ya na mai bada misali da bunƙasa harkar kiwon lafiya da ilimi da inganta matasa da suaransu a jihar.

Kazalika, Kwamishinan ya ƙara da cewa, ƙin bin tsarin doka da APC ke bayyanawa su suka sanya al’umma ta ƙaurace mata, ya na mai cewa gwamnatin Abba za ta cigaba da zuba ayyukan ci-gaba a jihar don amfanin al’umma.

By Babaji