Sarautar SARKIN BAI sarauta ce daɗɗiya kuma babba wadda ta samo asali daga Kano. Akwai ruwayoyi guda biyu akan asalin sunan wannan sarauta maganar farko ita ce sarautar SARKIN BAI sarauta ce ta kakanni.
An fara yinta tun zamanin Sarkin Kano Muhammadu rumfa wanda ya yi mulki 1463 zuwa 1499 kamar yadda bayani yagabata cewa sarkin Kano rumfa shi ne ya fara yin sarautar babanni, kuma a cikin waɗanda yana da akwai Sarkin Bai to tun daga wannan sarauta aka samu wannan suna abinda sarkin bai take nufi a wannan ruwaya shi ne SARKIN BAYI wato shugaban dukkan bayin sarki babanni, daga nan kuma ake cewa SARKIN BAI maimakon SARKIN BAYI a wata ruwayar.
Kuma an ce an samu wannan suna ne daga SARKIN BAYA yadda Abun yake shi ne dabon Danbazau ya aikawa sarkin Musulmi yana neman sarautar Kano bayan rasuwar Sarkin Kano Sulaimanu, sai aka ce masa an riga an bada sarauta amma sarkin Musulmi ya yi masa alƙawarin cewa idan wanda aka bai wa sarauta ya riga daban Danbazau rasuwa za a bashi sarauta to daga wannan lokacin ake kiran dabon Danbazau da sunan SARKIN BAYA to wannan shi ne asalin sunan wannan sarauta a wannan ruwayar to daganan kuma ta koma sarkin Bai Sarautar SARKIN BAI tana cikin manyan sarautun Hakimai a Kano domin tana cikin tara ta Kano wanda ake cewa uku daidai da Sarki wato GALADIMA WAMBAI SARKIN BAI Kuma tana cikin masu zaɓen sarki tun zuwan Fulani gidan Fulanin jihadi wato Danbazawa sune suke wannan sarauta har yanzu.
Wannan sarauta ta Sarkin Bai ta yaɗu sosai a sauran masarautu ana yinta a matsayin Hakimi kuma ana yinta ga wanda suka dace da ita.
Kamar sauran sarautu ita ma wannan sarauta masartan faɗa suna yi mata take kirari dacewa GAIDA NAɗA WA SARKI GAIDA TAKARADA GORAU TUKUNYAR ƙARFE GAIDA TAKARAɗA IRIN HABUBA IRIN ZAILANI GAIDA TAKARADA BAREBARI DAGA BARNO TAKARADA KALWA SUKA KAWO.
Daga ZAUREN DAGA MASARAUTUNMU.07039217236.
