CBD ya umarci bankuna su wallafa asusun da aka rufe da kuɗaɗen da ba a neme su ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗaɗe da su bayyana wa al’umma asusun da aka rufe da kuɗaɗen da aka bar su kara zube da wasu kadarorin kuɗi a shafukan yanar gizo.

Hakan na ƙunshe ne a wata takarda ɗauke da sanya hannun jami’i Michael Akuka a madadin Daraktan Ɓangaren Tsare-tsaren Kuɗi da gudanar da su na bankin.

Umarnin ya buƙaci cibiyoyin kuɗaɗen da su wallafa sunayen mutanen da ke da asusun da aka rufe da irin asusun da kuma wajen da aka buɗe asusun.

Ya ce, yayin da aka samu wata cibiya da ba ta da shafin yanar gizo, wajibi ne ta yi hakan ta shafin ƙungiyar da ta ke ƙarƙashinta.

Haka kuma, lallai ne sai an wallafa bayanan aƙalla sau ɗaya a shekara a manyan gidajen jaridu na ƙasa guda biyu da wallafa su a manyan ofisoshin jihohi da rassan ƙananan bankuna.

La’akari da yiwuwar taka dokokin sirrin masu asusu, CBN ya kafa hujja da layi na 25(b) na dokar ɓoye bayanai ta NDPA ta 2023 da ke sassauci akan bayyana wasu sirrika, waɗanda daga ciki akwai na kuɗaɗen da masu su ba su nema ba.

Kwararru kan ɓoye bayanan sirri da masu sharhi akan kuɗi sun samu mabanbanta ra’ayoyi game da matakin ganin yadda wasu ke ganin hakan a matsayin amfana da bayyana kuɗaɗen a fili, yayin da wasu ke gargaɗin yiwuwar fuskantar haɗarin bayyana sirri.

By Babaji